Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Amurka Zata Hana Kwankwaso Shiga Kasar
Published: February 11, 2026 at 1:28 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka guda biyar daga jam’iyyar Republican sun gabatar da kudiri a majalisar wakilai ta ƙasar domin tilasta wa sakataren harkokin wajen Amurka gabatar da cikakken rahoto kan matakan da ƙasar ke ɗauka wajen magance zargin tsananta wa addini da kisan gilla da ake cewa na faruwa a Najeriya.

Idan kudirin ya zama doka, ana sa ran ma’aikatun harkokin waje da baitulmali na Amurka za su kakaba takunkumi, ciki har da hana biza da kwace kadarori, kan “mutane ko ƙungiyoyin da ke da hannu a take ‘yancin addini” a Najeriya.

Wadanda aka ambata a cikin kudirin domin yi musu takunkumi sun haɗa da tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) Miyetti Allah Kautal Hore da kuma waɗanda aka bayyana a matsayin “makiyayan Fulani masu ɗauke da makamai a Najeriya.”

Kudirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan batun tsaro da rikice-rikicen addini a Najeriya.

Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa daga waɗanda aka ambata kan wannan mataki da aka gabatar a majalisar dokokin Amurka.

Amurka, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Farfesa Inuwa Ja’afaru Yakarbi Ragamar Shugabancin Jami’ar Kashere
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Nada Shugaban NAHCON

Karin Labarai Masu Alaka

Tattalin Arzikin Kasar Uganda Zai Bunkasa A Wannan Shekarar Labarai
Hukumar MDD Tace Wadanda Suka Mutu A Harin Sudan Sun Haura 70 Afrika
Gidauniya: An Fara Tiyatar ‘Hernia’ Da ‘Hydrocele’ Kyauta A Jihar Katsina Labarai
Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Afrika
Tinubu Ya Bayyana ‘Yan Bindiga Da Cewa Ruwa Yakarewa Dan Kada Afrika
Hamas Ta Kwance Damara Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yau Shekaru 60 Da Kisan Gilla Ga Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
  • Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutum 1 Yayinda Mutane 11 Suka Kamu A Jihar Gombe Najeriya
  • PDP Ta Nemi Bincike Kan Rushewar Ginin Majalisar Dokokin Gombe, Tayi Zargi Game Da Sakaci Labarai
  • Mutane 13 Sun Mutu Inda Wasu 57 Suka Jikkata A Barundi Afrika
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Labarai
  • Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau Ya Koma Jam’iyyar APC Afrika
  • Shugabannin Darikar Anglican Sun Bada Sanarwar Kafa Sabuwar Majalisa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.