Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yace ya zanta da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, ya kuma jaddada masa muhimmancin lafa rikici yayin tattaunawar tsagaita wuta a Pakistan.
Ba tabbacin ci gaba a tattaunawar sulhu
A cikin mabanbantan rahotanni da kafafen yada labarai daga jami’ain a Amurka da Iran, ya nuna cewa kasashen biyu basuyi kusa da cimma matasaya ba.
Kafin a fara tattaunawa, wani babban jami’i a Iran ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Amurka ta yarda da zata saki kadarorin Iran da aka rike a Qatar da sauran bankunan dake wasu kasashe. Amma wani jami’in Amurka nan da nan ya musanta hakan.
Banda sakin kadarorin ta dake kasashen waje, fadar gwamnatin Tehran ta bukaci da ta mallaki ikon tafiyar da mashigin ruwa na Hormuz, da biyan diyyar yaki da kuma tsagaita wuta a yankin baki daya har da a kasar Lebanon a cewar jami’ai da kafar talabijin ta Iran.
A nasa bangaren bukatun da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar sun sha banban, mafi karancin su yace yana son a rika gudanar da wucewa da kayayyaki ta mashigin ruwan na Hormuz daga ko ina a duniya ba tare da fuskantar kalubale ba, da kuma dakile shirin makamashin nukiliya na Iran domin a tabbatar bazata iya hada atomic bomb ba.
Isra’ila, wadda ta hadu da Amurka wajen kaiwa Iran hari a yakin da aka fara shi ranar 28 ga Watan Fabrairu, ta kuma kasance tana sakarwa ‘yan kungiyar Hezbollah da Iran ke marawa baya bama-bamai a kasar Lebanon, ta kuma ce yakin da ake a Lebanon baya cikin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran.


