Sojoji sun kashe ’yan bindiga da suka yi wa ’yan kasuwa kwanton-bauna a Sabon Birni.
Sojoji sun kashe akalla ’yan bindiga 13 a Sabon Birni, Jihar Sakkwato, bayan sun kai dauki ga ’yan kasuwar da aka yi wa kwanton-bauna a hanyar Tarah–Karawa da safiyar Litinin.
’Yan bindigar sun tare ’yan kasuwar ne da misalin 8:00 na safe a Kwanan Akimbo, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako ta Sabon Birni, Sojojin da ke Kurawa sun yi gaggawar isa wajen, inda suka yi musayar wuta da maharan na kusan sa’a guda kafin su fatattake su.
An gano gawarwakin maharan tara a wurin, a yayin da aka gano wasu hudu a cikin daji kusa da rafin.
Sojojin sun kwato makamai da babura da dama, yayin da dukkan ’yan kasuwar aka ceto su cikin koshin lafiya, in banda fararen hula biyu da suka ji rauni.
- Babu asara daga bangaren sojoji, kuma mazauna Kurawa da makwabta na murnar nasarar aikin wani dan majalisar jiha, Aminu Boza, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa bincike na cigaba domin gano sauran maharan.
Harin ya faru ne kwana guda bayan kashe mutane bakwai da sace mata da dama a Gatawa da Shalla da ke yankin.


