Za Iya Juyin Juya Hali A Najeriya In A Ka Cigaba Da Take Hakkin Dan’adam -Inji Atiku Abubakar Kan Yunkurin Kama Elrufai
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi gargadin za a iya samun juyin jiuya hali matukar a ka cigaba da take hakkin jama’a na Dan’adam.
Alhaji Atiku Abubakar na magana ne a ziyarar jaje da ya kai wa tsohon gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai wanda jami’an hukumar Efcc su ka yi yunkurin kama shi bayan dawowa daga tafiya a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe a Abuja.
“Ka rike manyan mukamai a kasar nan, ka yi minister, ka yi gwamna kuma ka sauke nauyin da ka ke kanka. Ba bukatar zubar ma ka da mutunci, domin zubar ma ka mutunci tamkar zubar da mutuncin dukkan ajin ‘yan siyasa ne” Inji Atiku Abubakar.
A nan Atiku wanda jigo ne a sabuwar jam’iyyar hadaka ta ADC da Elrufai ke ciki, ya yi gargadin irin wannan yunkuri da ya zayyana da take hakkin Dan’adam ke iya haddasa juyin juya hali.
Kamar sun hada baki da Elrufai kan batun jiran Elrufa’in ya dawo gida gabanin daukar wani mataki ta hanyar mika ma sa takardar gayyata a hukumance maimakon yunkurin cafke shi kenan ta wannan hanyar aiki da cikawa.
Jama’a dai tun farko sun yi dafifi su ka hana jami’an Efcc yunkurin kama Elrufai cewa hakan ba zai yiwu ba sai an bi ta hanyar da su ke ganin ta dace.
Tsohon gwamnan ya yi wata magana da wasu ke ganin ta wuce yanayin wani dan kasa gama-gari ya iya fada ya kwana lafiya yayin da ya shaidawa jami’an Efcc ko shugaban kasa ba zai fada ma sa abun da zai yi ba “ko shugaban kasa ba zai fada mi ni abunda zan yi ba
Hukumomi dai sun amshe fasfo din Elrufai kuma da alamu zai amsa gayyatar Efcc a tsanake.
Hukuamr ta yaki da cin hanci ta sha nanata ba ta daukar mataki kan wani haka kawai sai ta samu hujjoji kwarara.
Kakakin hukumar Dele Oyewole na cewa Efcc na hukunta mutane kan laifinsu ba don wata wariya ko tsana ba.
In za a tuna shi ma tsohon ministan shari’a Abubakar Malami ya samu kansa a wannan dambarwa bayan samun beli daga kotu amma jami’an DSS su ka sake awun gaba da shi.
Ga Rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya Daga Abuja


