Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ba Mu Goyon Bayan Kowane Dan Takara A 2027 – ASUU Afrika
  • Wakilai Daga Ƙasashen Duniya Za Su Halarci Taron Hulɗa Da Jama’a A Abuja Afrika
  • Pasto Buru Ya Karrama Malamin JNI Kan Ƙoƙarin Samar Da Zaman Lafiya A Arewacin Najeriya Afrika
  • An Kashe Shugaban Fulani Makiyaya A Najeriya Afrika
  • Afirka Na Bukatar Adalci Da Tallafin Kuɗi Wajen Yaƙi Da Sauyin Yanayi – ACR Afrika

Tinubu Ya Shiga Cikin Ka’aba Ya Yi Addu’a
Published: November 2, 2026 at 7:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da kokarin gina kasa mai wadata, tare da karfafa tattalin arziki, zuba jari a makomar matasa da kuma aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’ummar kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin da yake tsokaci kan ziyarar ibadar Umara da ya kai kasar Saudiyya, inda ya samu damar shiga cikin dakin Ka’aba mai alfarma da ke birnin Makkah domin gudanar da addu’a.

Tinubu ya nuna godiyarsa ga Mai Kula da Harami Biyu Masu Alfarma, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, bisa damar da suka ba shi da sauran tawagarsa ta Najeriya na shiga cikin Ka’aba domin yin addu’a.

Ya bayyana wannan dama a matsayin wata babbar karamci mai tarihi da ba zai taba mantawa da ita ba, yana mai cewa hakan na kara tabbatar da kyakkyawar dangantaka, zumunci da hadin kai tsakanin Najeriya da Saudiyya.

Shugaban ya ce ya yi amfani da wannan dama wajen rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi hikima da juriyar da za su taimaka masa wajen ci gaba da yi wa al’ummar Najeriya hidima yadda ya kamata.

A cewarsa, damar jagorantar Najeriya a matsayin Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin kasar wata babbar ni’ima ce daga Allah, wadda wajibi ne ya rama ta ta hanyar jajircewa wajen yi wa kasa hidima.

Haka kuma, Tinubu ya yi tsokaci kan sakon da ke cikin Alkur’ani mai girma, musamman Suratu Ali Imran, aya ta 26, wadda ta bayyana cewa Allah Madaukakin Sarki ne mamallakin mulki da iko, Yana ba wa wanda Ya so mulki, kuma Yana karbe shi daga wanda Ya so.

Ya jaddada cewa wannan koyarwa na nuna cewa dole ne shugabanni su gudanar da mulki cikin tawali’u, amana da kuma kishin al’ummar da suke jagoranta.

Shugaban ya kara da cewa aniyarsa ta gina Najeriya, wadda ya kira Project Nigeria, ta kara karfi, yana mai tabbatar da kudurinsa na ganin kasar ta samu ci gaba da wadata bisa yardar Allah da kuma bukatun al’ummar kasar.

Dangane da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, Tinubu ya bayyana kyakkyawan fata kan makomar tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa an gina tubali mai karfi, kuma kasar na samun ci gaba bayan tsallake wani mawuyacin yanayi na tattalin arziki.

Ya kuma jaddada muhimmancin zuba jari a makomar matasa, yana mai cewa matakan da shugabannin yau suka dauka za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance irin tarihin da al’ummomi masu zuwa za su tuna da su.

Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen karfafa tattalin arziki, samar da damarmaki ga matasa da kuma gina yanayin da zai bai wa ‘yan Najeriya damar cimma burinsu.

A wani bangare kuma, Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, da Ministan Kula da Lafiya da Jin Dadin Al’umma, Ali Pate, tare da gwamnonin jihohin Borno, Sokoto, Jigawa, Kaduna, Yobe da Kwara, da wasu manyan ‘yan kasuwa, sun nuna godiyarsu ga Allah bisa damar da suka samu na shiga cikin Ka’aba tare da gudanar da addu’a.

Daga cikin ‘yan kasuwar akwai Shugaban Kamfanin BUA Group, Abdulsamad Rabiu, da Babban Jami’in Kamfanin Oando, Wale Tinubu.

Wannan bayani na Shugaban Kasa na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Kishin Al’ada: Ministan Kamaru Mohamadou Moustafa Da Gudunmawarsa Ga Hausawa
Next Post: Nijar Da Gabashin Libya Sun Kulla Yarjejeniya

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen AES Sun Buɗe Gidan Talabijin Na Bai Daya Afrika
‘Yansandan Uganda Sun Tsare ‘Yar Fafutukar Kare Hakkin Bil’adama Sarah Bireete Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan Sandan Gombe Sun Yi Taron Gaggawa Da Jam’iyyun Siyasa Da INEC Kan Tsaro Labarai
Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai
Koriya Ta Arewa Ya Goyi Bayan Iran Wajen Zaben Sabon Jagora Mojtaba Khameni Afrika
CP Chuso Ya Buƙaci Al’ummar Gwani Su Haɗa Kai Da ’Yan Sanda Wajen Yaƙi Da Laifuka Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ba Mu Goyon Bayan Kowane Dan Takara A 2027 – ASUU
  • Jami’in NSCDC Ya Harbe Direban Tirela A Gombe
  • Wakilai Daga Ƙasashen Duniya Za Su Halarci Taron Hulɗa Da Jama’a A Abuja
  • Pasto Buru Ya Karrama Malamin JNI Kan Ƙoƙarin Samar Da Zaman Lafiya A Arewacin Najeriya
  • An Kashe Shugaban Fulani Makiyaya A Najeriya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi Labarai
  • Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
  • Gombe Ta Yi Kira Ga Jami’o’i Su Tallafa Wa Gwamnati Ta Hanyar Bincike Da Ƙirƙire-ƙirƙire Afrika
  • Barcelona na hangen Enrique Ko Arteta Wasanni
  • ‘Yan Sanda A Gombe Sun Jaddada Shirin Yaƙi Da Munanan Dabi’u Afrika
  • Kasar Rasha Ta Zargi Ukraine Da Kai Hari Gidan Shugaban Rasha Amurka
  • Mutum Mafi Tsufa A Saudiyya Ya Rasu Yana Da Shekaru 142 Labarai
  • ’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.