Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara aiwatar da shirin tallafin kuɗi na kowane wata, inda za ta riƙa bai wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi Naira 50,000 domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.
Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Doro ya ce shirin mai suna National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI), wani shiri ne na Shugaban Ƙasa da aka ƙaddamar domin samar da tallafin kuɗi na gaggawa ga miliyoyin ‘yan Najeriya masu fama da matsin tattalin arziki.
Ya bayyana cewa an ƙaddamar da shirin ne sakamakon hauhawar farashin kayan abinci a duniya da kuma tsadar kayayyakin masarufi, lamarin da ke ƙara jefa iyalai cikin matsin rayuwa.
Ministan ya ce, a ƙarƙashin shirin, waɗanda suka cancanci cin gajiyar tallafin za su riƙa karɓar Naira 50,000 duk wata domin taimaka musu wajen biyan buƙatun yau da kullum da kuma rage musu nauyin tsadar rayuwa.
Ya ƙara da cewa za a riƙa duba shirin lokaci zuwa lokaci bisa la’akari da sauye-sauyen farashin kayayyaki da tsadar rayuwa, inda za a sanar da waɗanda suka cancanci tallafin kai tsaye kafin duk wani sauyi.
A cewarsa, ma’aikatar tana aiki tare da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet da aka amince da su domin tabbatar da cewa ana isar da kuɗaɗen cikin aminci, kan lokaci da kuma gaskiya.
Doro ya bayyana cewa waɗanda suka cancanci tallafin za su riƙa samun saƙonnin tes daga kamfanonin da za su gudanar da biyan kuɗin, inda za a buƙaci amincewarsu kafin a tura kuɗin kai tsaye zuwa asusun bankinsu ko walat ɗin wayoyinsu.
Ministan ya jaddada cewa babu buƙatar mutum ya cike takardar neman tallafi, ya biya wani kuɗi ko ya yi rajista ta hannun wani wakili kafin ya amfana da shirin.
Ya kuma gargaɗi ‘yan Najeriya da su yi hattara da masu damfara, yana mai ba da shawarar kada kowa ya bayyana lambar sirrinsa ta ATM (PIN) ko lambar tantance asusun bankinsa (BVN) ga wani mutum saboda neman tallafin.


