Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Shari’ar Sirika: Odofin Ya Sha Tambayar Kwakwa Afrika
  • Ana Tsanmmanin Tinubu Ya Shiga Ka’aba Don Ganawa Da Allah Afrika
  • Amupitan Ya Gargadi Jami’an INEC Kan Cin Hanci Afrika
  • Keke NAPEP Ta Kashe Yara Biyar, Wasu Uku Rai Kwakwai Afrika
  • Ƙungiyar Ansaru Ta Dauki Alhakin Kashe Masussuka Afrika

‘Yan Jarida Sun Samu Horo Kan Tantance Labaran Kanzon Kurege
Published: October 31, 2026 at 4:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

An buƙaci ‘yan jarida da su taka muhimmiyar rawa wajen inganta rahotannin zaɓe cikin harsunan ƙasa daban-daban, domin rage matsalolin fassara, yaɗa labaran ƙarya da tabbatar da cewa kowane ɓangare na al’umma ya samu sahihin bayanai gabanin babban zaɓen shekarar 2027 a Najeriya.

An bayyana hakan ne a yayin wani horon kwanaki uku da aka shirya wa ‘yan jarida a kan dabarun ƙarfafa ƙwarewa, jagoranci da bunƙasa fasahohi wajen yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya, tantance sahihancin labarai da kuma amfani da basirar na’ura mai kwakwalwa (AI).

Taron wanda ya samu halartar ‘yan jarida daga jihohin Arewacin Najeriya da suka haɗa da Filato, Benuwai, Taraba, Katsina, Abuja, Yola, Kano, Bauchi da Kaduna, da sauransu, an gudanar da shi ne a Comfort Hub Hotels and Suites, Nassarawa GRA, a jihar Kano Najeriya

An shirya horon ne a ƙarƙashin shirin tallafawa ECOWAS kan zaman lafiya, tsaro da shugabanci (EPSG), tare da goyon bayan Tarayyar Turai (EU), Ma’aikatar Harkokin Waje ta Denmark da kuma Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Jamus.

Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a horon shi ne gibin da ake da shi wajen amfani da basirar na’ura mai kwakwalwa (AI) a harsunan ƙasa, musamman ƙarancin bayanan da ake da su a yanar gizo, bambancin yarukan yanki, kura-kuran gane magana da kuma rashin fahimtar al’adu.

An kuma jaddada cewa bayanan ƙarya na iya yaɗuwa cikin sauri ta harsunan da al’umma suka saba da su, musamman ta hanyoyin sadarwa da mutane suka amince da su, yayin da yawancin binciken tantance sahihancin labarai ake wallafawa da Turanci a shafukan yanar gizo, wanda hakan ke hana saƙon kaiwa ga ainihin mutanen da suka fara karɓar labarin ƙaryar.

A ƙarshe, an buƙaci mahalarta horon da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen rage matsalolin harshe, ƙarfafa amfani da harsunan ƙasa wajen yaɗa sahihan bayanai, da kuma tabbatar da samun damar sadarwa, amincewa, bayar da shawarwari da kuma halartar kowane ɓangare na al’umma a harkokin jarida.

An bayyana cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa aikin jarida da tabbatar da cewa dukkan al’ummomi sun samu sahihan bayanan zaɓe cikin harshen da suka fahimta gabanin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Kwamitin Tsaftar Muhalli A Gombe Zai Dauki Mataki Kan Masu Babura Da Keke Napep

Karin Labarai Masu Alaka

Kotun Gombe Ta Horas Da Lauyoyi Kan Sabon Tsarin Rijistar Takardun Rantsuwa Afrika
Amurka Ta Kai ‘Yan Cirani Kamaru Afrika
GOSEMA Ta Horar Da Mambobin LEMCs A Jihar Gombe Afrika
An Samu Bullar Cutar COVID 19 A Najeriya Afrika
Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800 Labarai
Najeriya: Ba Don Leken Asiri Muka Tura Jirgin Yakin Mu Ba Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Jarida Sun Samu Horo Kan Tantance Labaran Kanzon Kurege
  • Kwamitin Tsaftar Muhalli A Gombe Zai Dauki Mataki Kan Masu Babura Da Keke Napep
  • INEC Ta Amince Da Pantami Da Gwarzo Su Ci Gaba Da Takarar Gwamna
  • Ahmed Gara Ya Dakatar Da Ayyukan Tallafa Wa Al’umma A Gombe
  • Shari’ar Sirika: Odofin Ya Sha Tambayar Kwakwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • INEC Mayar Da Lokacin Zaɓen 2027 Kafin Azumi Najeriya
  • APC Ta Sauya Jerin ‘Yan Takararta Bayan Nazarin Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Fidda Gwani Afrika
  • Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
  • Maharan Bindiga Sun Kashe Mutane 12 Masu Hakar Ma’adanai A Jihar Filato Labarai
  • Kasashen Cambvodia Da Thailand Sun Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsaro
  • Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Matsalar Tsaro A Shiyar Labarai
  • An Saka Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Lamurde Jihar Adamawa Tsaro
  • Maulidi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.