Daga Mohamman Awwal Garba a Kamaru
A ci gaba da haska fitattun ‘yan asalin Hausawa da suka yi fice a kasar Kamaru, an karkata haske kan Mai Girma Mohamadou Moustafa, Minista kuma Mataimakin Sakatare-Janar a Fadar Shugaban Jamhuriyar Kamaru, wanda ya shahara wajen hidimtawa kasarsa da kuma bayar da gudunmawa wajen bunkasa al’adun Hausawa.
Mohamadou Moustafa, wanda ya fito daga garin Banyo da ke yankin Adamawa na kasar Kamaru, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yan asalin Hausawa da suka samu nasarar kaiwa manyan mukamai a gwamnatin kasar ta hanyar kwazo, kwarewa da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
Doguwar tafiya a hidimar kasa
Tun bayan shiga aikin gwamnati a shekarar 1990, Mohamadou Moustafa ya samu horo da ilimi a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Kamaru, IRIC, da kuma babbar makarantar koyon tattalin arziki da kimiyyar siyasa ta Landan, wato London School of Economics and Political Science.
A tsawon rayuwarsa ta aikin diflomasiyya, ya rike mukamai daban-daban, ciki har da Sakatare na Biyu a Ofishin Jakadancin Kamaru da ke Legas, Najeriya, sannan ya yi aiki a matsayin Sakatare na Farko a ofishin jakadancin kasar da ke Landan na tsawon shekaru tara.
Bayan haka, ya koma Ma’aikatar Harkokin Wajen Kamaru, inda ya kula da harkokin Asiya da kuma hulda da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC).
Kwarewarsa a harkokin diflomasiyya da mu’amala da kasashen duniya ta taimaka wajen samun karin daukaka, inda a halin yanzu yake rike da mukamin Minista kuma Mataimakin Sakatare-Janar a Fadar Shugaban Kasa, yana taka muhimmiyar rawa a tafiyar da harkokin gwamnatin Shugaba Paul Biya.
Mai kishin al’adun Hausawa
Baya ga nasarorin da ya samu a aikin gwamnati da diflomasiyya, Mohamadou Moustafa ya kuma kasance mai kishin al’adun Hausawa, tare da bayar da gudunmawa wajen kare su da kuma ganin an bunkasa su a kasar Kamaru.
Ya halarci kuma ya taka muhimmiyar rawa a wasu manyan shirye-shiryen al’adun Hausawa, ciki har da taron Bakandamiya na shekarar 2017 da kuma Festi Haoussa na shekarar 2018.
Haka kuma, an bayyana irin goyon bayan da yake bai wa ayyukan bunkasa al’adun Hausawa a lokacin da ya wakilci Shugaban Kamaru, Mai Girma Paul Biya, wajen kaddamar da Cibiyar Al’adun Hausawa.
Wannan mataki ya nuna muhimmancin da yake bai wa al’adun Hausawa da kuma rawar da yake takawa wajen hada kan al’umma da hukumomin gwamnati domin tabbatar da dorewar wannan muhimmiyar gadon tarihi.
Abin alfahari da abin koyi ga matasa
Tarihin rayuwar Mai Girma Mohamadou Moustafa ya nuna cewa asalin mutum ba ya zama shamaki ga samun nasara, matukar yana da ilimi, jajircewa, gaskiya da kishin kasa.
Daga garin Banyo zuwa manyan ofisoshin gwamnatin Kamaru, tafiyarsa ta zama abin koyi ga matasa, musamman masu sha’awar shiga aikin gwamnati, diflomasiyya da kuma kare al’adunsu.
Gudunmawarsa ga ci gaban kasar Kamaru da kuma kokarinsa na ganin an kiyaye al’adun Hausawa sun sanya shi cikin mutanen da al’ummarsu ke alfahari da su.
Labarinsa ya zama wata muhimmiyar shaida ta yadda ilimi, kwarewa da sadaukarwa za su iya bude wa mutum kofofin samun nasara tare da ba shi damar yi wa kasa da al’ummarsa hidima.


