Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna
Published: March 31, 2026 at 5:01 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi Allah-wadai da kakkausar murya game da hare-haren rashin imani da wasu ‘yan bindiga suka kai a gundumar Angwan Rukuba da ke Jos, Jihar Filato, da kuma kauyen Kahir da ke Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.

Shugaban ya bayyana wadannan hare-hare, wadanda suka hada da kisan jama’a a Jos da kuma garkuwa da baki ’yan bikin aure a Kaduna, a matsayin babban kalubale ga hadin kan Najeriya. Ya kuma tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba za a zura ido wadanda suka aikata wannan danyen aikin su sha da dadi ba.

A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa kan fannin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana maharan a matsayin azzalamai kuma matsorata.

Shugaba Tinubu ya ba wa jami’an tsaro umarnin su kara kaimi wajen kamo wadanda suka aikata laifin da kuma wadanda ke yada labaran karya da nufin ruruta wutar rikici. Haka kuma, ya ja kunnen wasu bangarorin kafafen yada labarai da ke kokarin danganta hare-haren da batun addini.

Kiran Jami’an Tsaro: Ya bukaci jami’an tsaro su rika amfani da bayanan sirri don dakile hare-hare kafin su auku.

Ceton Wadanda Aka Sace: Ya ba da umarnin gaggauta ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a kauyen Kahir.

Kayayyakin Aiki: Ya bayyana cewa gwamnati na kan hanyar sayo manyan makaman zamani don bin sawun miyagun mutane a duk inda suke.

Shugaban ya jinjina wa Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa kokarinsu na shawo kan lamarin da kuma tallafawa ayyukan ceto.

Daga karshe, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da suka rasa rayukansu, sannan ya yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata, yana mai kira ga al’umma da su ba wa jami’an tsaro hadin kai don tabbatar da zaman lafiya.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Yusuf Gawuna Ya Koma Jam’iyar ADC
Next Post: Sakataren Tsaron Amurka Yace Yaki Tsakanin Amurka Da Iran Zai Dauki Sabon Salon

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Trump Ya Amince Da Tsawaita Cinikayya Tsakanin Amurka Da Kasashen Afirka Afrika
Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa Afrika
Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa Afrika
Ana Kokarin Dawo Da Wutan Lantarki A Cuba Afrika
Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Harin Jos Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Baital Malin Amurka Tace Sahannun Trump Zai Fito A Kudin Kasar Amurka
  • Sanyi Mai Tsanani Da Dusar Kankara Ya Tsaida Al’amura A Amurka Amurka
  • Jam’iyar APC A Jihar Gombe Ta Tsayar Da Jamilu Isiyaku Gwamna Takarar Gwamna Afrika
  • An Bude Kamfanin Sarrafa Ma’adanai A Kasar Mozambique Labarai
  • Trump Da Bin Salman Da Wasu Kasashe Za Su Sa Hannu A Rikicin Sudan Labarai
  • Kungiyar MDD Ta Bukaci Ayi Bincike Game Da Kashe ‘Yan Iran Sauran Duniya
  • Gwamnan Gombe Ya Yaba Da Hikima Da Jagorancin Sarkin Gombe A Shekaru 12 Na Jagoranci Afrika
  • Shugaban Amurka Yace Zasu Kakabawa Mashigar Hormuz Takunkumi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.