Jam’iyyar APC da Shugaba Bola Tinubu sun fara aiwatar da wata babbar dabarar siyasa domin tabbatar da nasara a zaben shugaban kasa na 2027, ta hanyar karfafa ikonsu a yankunan Kudu da Arewa ta Tsakiya.
Majiyoyi daga APC sun ce an fara shirin tun fiye da watanni biyar da suka wuce, bayan rahotannin sirri sun nuna yiwuwar barazana daga Arewa da kuma bullowar hadakar jam’iyyun adawa.
Shirin na da nufin rage tasirin adawar Arewa ta hanyar samun dunkulen kuri’u daga Kudu da Arewa ta Tsakiya.
Kungiyoyin Arewa da wasu fitattun ‘yan siyasa sun nuna rashin jin dadi da mulkin Tinubu, lamarin da ya sa APC ke kokarin karbe dukkan jihohin Kudu a 2027.
A zaben 2023, jam’iyyun adawa sun lashe jihohi da dama a Kudu da Arewa ta Tsakiya, ciki har da Lagos da Abuja.
APC ta ce tana amfani da kulla kawance, jawo hankalin manyan jiga-jigai da kuma tasirin gwamnatin tarayya domin kwato wadannan jihohi.
Jam’iyyar ta yi imanin cewa samun cikakken goyon bayan Kudu zai bai wa Tinubu gagarumar dama ta lashe zabe wa’adi na biyu.


