Shugaban Amurka Donald Trump yayi kira ga ‘yan kasar Iran su ci gaba da zanga zanga, dauki yana tafe, yayinda shugabanin addinin kasar suke ci gaba da daukan matakan murkushe zanga zanga mafi girma da kasar ta fuskanta cikin shekaru masu yawa.
“Yan kishin kasa a Iran, ku ci gaba da zanga zanga, ko kwace iko a hukumomin mu, dauki ko taimako yana nan tafe, shugaban na Amurka ya fada a shafinsa na Truth Social. Ya kara da cewa, ya soke duk wata ganawa da jami’an Iran har sai an kawo kashen kashen rayuka masu zanga zanga da bashi ma’ana.
Zanga zangar wacce matsalolin tattalin arziki suka haifar, itace kalubale daga cikin gida mafi tsanani da shugabannin Iran a suka fuskanta cikin shekaru uku da suka gabata, kuma yana zuwa ne yayinda kasar take kara fuskantar matsin lamab da ketare, bayanda Isra’ila da Amurka suka kaiwa kasar farmaki a bara.
Bayanda shugaba Trump ya wallafa kiran da ya yi wa ‘yan kasar ta Farisa, shugaban hukumomin tsaro a Iran Ali Larijani, ya fada ta shafinsa a X cewa, PM Isra’ila da da shugaba Trump sune manyan masu kashe ‘yan kasar.
A karon farko tunda aka fara zanga zanagar cikin mako biyu, hukumomin kasar sunce an kashe mutane 2000.


