Tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, Justice Tanko Muhammad, ya rasu.
Rahotanni sun nuna cewa Allah ya karbi rayuwarsa ranar talata, inda ake ci gaba da nuna jimami da addu’a daga fannonin daban-daban na kasar.
Justice Tanko Muhammad Dan Asalin garin Giade a jihar Bauchi ya rike mukamin Chief Justice na Najeriya daga shekarar 2019 zuwa 2022 kafin ya ajiye aiki saboda dalilan lafiya.
‘Yan Najeriya da dama sun bayyana alhini tare da rokon Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa, ya sa Aljanna Firdaus ta kasance makomarsa.
Za a ci gaba da samun karin bayani daga hukumomin shari’a da iyalansa.


