Dazu da maraicen nan agogon Najeriya kotun koli ta kasar Brazil ta kammala bin bahasin shari’ar da aka yi ma tsohon shugaba Jair Bolsanaro game da yunkurin yin juyin mulki, abinda ya share fagen tasa keyarsa zuwa kurkuku domin ya fara zaman shekaru 27 da aka yanke masa a shari;ar.
Kotun, wadda ta ki yarda da daukaka karar da Bolsanaro yayi a baya cikin wannan watan, ta ce har yanzu ba ta da cikakken bayani na lokacin da tsohon shugaban zai fara zaman hukumcin daurin da aka yanke masa.
Ta hanyar kammala wannan bin bahasi a yau, mai shari’a ALexandre de Moraes ya tabbatar da wannan hukumci na daurin shekaru 27 a kan Bolsanaro.


