Wakilan Rasha da Ukraine sun gana jiya Jumma’a a Abu Dhabi, domin shawarwari kan batu mafi sarkakiya watau muhalli ko yankin kasa. Kuma babu alamun samun daidaito yayinda wani harin da Rashar ta kai wa ukraine ya jefa kasar cikin duhu fiye da ako wani lokaci tunda aka fara wannan yaki kusan shekaru hudu yanzu.

Hukumomi dake birnin Kyiv na Ukraine suna fuskantar matsin lamba daga Washington cewa ta cimma yarjejeniya da Moscow na kawo karshen yakin da Rasha ta afka mata cikin watan Febureru na shekarar 2022. Moscow ta dake tilas wa ukraine ta sallama mata illahirin gabashin kasar mai arzikin masana’antu da ake kira Donbas, kamin ta amince ta daina yakin.
“Abu mafi muhimmanci shine Rasha ta amince ta kawo karshen wannan yaki da ta fara,” shugaban Ukraine Zelensky ya fada, a wata sanarwa da ya wallafa a shafin Telegram, ya kara da cewa yana ci gaba da tuntubar wakilan Ukraine a zauren shawarwarin, duk da haka yace da wuya ace ga makomar shawarwarin da ake sa ran kawo karshe wunin Asabar.


