‘Yan sanda a tarayyar tsibiran Bahamas sun fada dazu cikin daren nan cewa sun kama mijin wata mata ba Amurkiya wadda ta bace daga wani kwalekwale a kasar.
Hukumomi sun ce an kama mutumin mai shekaru 59 a tsibirin Abaco, ana yi masa tambayoyi. Wani kakakin rundunar tsaron bakin tekun Bahamas ya fadawa kamfanin dillancin labaran AP cewa sun bude bincike game da aikata laifi a wannan lamarin.
‘Yan sandan ba su yi karin bayani ba, haka kuma ba su ce ko an tuhume shi da kisan kai ba.
Jami’ai suka ce matar mai suna Lynette Hooker, ‘yar shekaru 55 da haihuwa, tana tafiya tare da mijin nata a cikin wani kwale kwale mai tsawon kafa 8 daga Hope Town zuwa tsibirin ELbow Cay ranar asabar da daddare, sai mijinta ya fadawa hukumomi cewa ta fada cikin ruwa dauke da makullan jirgin, abinda ya sa sai injin wannan kwale kwale ya daina aiki.
Daga nan ne sai ya fadawa hukumomi cewa yayi amfani da hannunsa wajen ingiza kwalekwalen har zuwa bakin gaba inda ya fada ma wani abinda ya faru da safiyar lahadi.


