Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Wani Kauye A Jihar Sakkwato
Published: January 17, 2026 at 10:16 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 18, 2026

Mutane na ci gaba da tserewa daga gidajen su a kauyukan da ke jihar Sokoto sakamakon barazanar da ‘yan ta’adda suke musu.

Al’ummar karamar hukumar Isa sun koka kan yadda hare-haren ‘yan ta’addar yayi tsamari, tun bayan da shugaban wata kungiyar ‘yan ta’adda ya yi barazanar hallaka mazauna kauyen Tidibali, da yake zargin sun yi musu shune wajen jami’an tsaro, idan basu bar garin ba, ranar Jumu’ar da ta gabata.

Bello Turji ya far wa Tidibali, inda ya kashe mutane 3, kuma yayi gargadin idan ya sake dawowa kowaye ya tarar zai shaki lahira, don ko kaza ba zai bari ba.

Mazauna yankin sun ce wasu daga cikin ‘yan uwan su na tserewa kasar Nijar, ta bin hanyoyi masu matukar hatsari don su tsira da rayukan su.

Mutane da dama sun tsere zuwa kasar Nijar a cewar mazauna yankin, inda wasu suka kwashe iyalan su kaf, har da iyaye. Amma akwai wadanda sukai rashin sa’a, hukumomin Nijar suka kama su suka dawo da su Nigeria.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu Yayin Rikici A Uganda
Next Post: Trump Zai Sasanta Tsakanin Masar Da Habasha

Karin Labarai Masu Alaka

Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro Labarai
Sojojin Isra’ila Sun Kashe Babban Kwamandan Kungiyar Hezbollah Afrika
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 30 A Jihar Neja Najeriya
Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar Amurka
Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugabar Kungiyar Cinikayya Ta Duniya Ta Bukaci Kasashe Su Gyara Harkokin Cinikayya Afrika
  • Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
  • An Kaiwa Sojojin Ghana Hari A Lebanon Afrika
  • ECOWAS Zata Kafa Rundunar Yaki Da Rashin Tsaro Afrika
  • Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya Ta Bawa Gwamnan Kebbi Mukamin Kyautata Harkar Kiwo Najeriya
  • Shugaba Tinubu Yakarawa Mambobin ASUU Kashi 40 Na Albashi Najeriya
  • Akwai Bukatar Nazari Game Da Dangantakar Iran Da Kasashen Gulf Amurka
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.