A yayin da sanyi yayi tsanani a Gaza, ‘yan Palasdinu da suka rasa mazuguni, suna zuwa gidajen da Israela ta rusa ko wacce rana, inda suke ciro rodin karafa daga gine gine don amfani da su wajen kafa tantunan su, ko kuma su sayar don dogaro da kai.
Karafunan sun zama abubuwa masu daraja a Gaza, inda aka malkwaye su a rusassun ginunnukada sakamakon hare haren da sojojin Israela suka kai, inda gidaje kadan ne suka tsira.
Wasu daga cikin mazauna wurin su kan shafe kwanaki suna fasa ginin siminti mai kauri don fitar da karfen, yayin da wasu kuma suke shafe fiye da mako daya suna wannan aiki mai matukar wahala.
Aikin yana daukan lokaci me tsawo saboda kayan aikin da suke da shi ya tsaya ga kebura da guduma.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin yayi sandiyar samun tan miliyan 61 na rusassun gine-gine.


