Kakakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, yace an sako sauran dalibai 130 da aka sace daga wata makaranta ta ‘yan Katolika a jihar Neja, daya daga cikin sace-sacen mutane mafi muni da aka gani a kasar cikin ‘yan shekarun nan.
Bayo Onanuga ya fada cikin wata sanarwar da ya fitar a shafin X cewa an sako sauran dalibai 130 da ‘yan ta’adda suka sace, yana mai fadin cewa a yau litinin ake sa ran zasu isa Minna, babban birnin Jihar Neja, kuma zasu koma cikin ‘yan’uwansu domin suyi bukukuwan kirsimeti tare.
Mr. Onanuga yace daliban su samu ‘yan cinsu ne a bayan wani mataki na soja da jami’an leken asiri.
Daliban suna daga cikin yara fiye da 300 da malamai 12 da ‘yan bindiga suka sace daga makarantar St Marys Catholic dake garin Papiri da asubahin ran 21 ga waran Nuwamba.
Sace daliban ya haddasa fusata kan yadda rashin tsaro yake kara yin muni a yankin arewacin Najeriya, inda ‘yan bindiga ke kai hare-hare kan kauyuka da garuruwa da ma makarantu suna sace mutane don neman a biya su kudin fansa.


