Yeriman Ingila Harry ya maida martani kan sukar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa dakaru daga kasashe dake Kungiyar tsaro ta NATO, cewa sun kauracewa fagen yaki a Afghanistan. Yerima Harry yace irin sadaukar da kai da sojojin NATO suka yi a yakin nan Afghanistan, akwai bukatar ayi magana akai, a fadi gaskiya, tare da mutuntawa ko karrama rawar da suka taka.
A cikin wata sanarwa da ya bayar ranar Jumma’a, Yerima Harry, yace, nayi aikin soja a can. Na yi abota ta har abada a can. Yace Ingila kadai tayi hasarar dakaru 457.


