Ƙungiyoyin Gasar Premier 17 Za Su Rasa ‘Yan Wasa 40 saboda Gasar Cin Kofin kasashen Afirka AFCON 2025
Kofin Kasashen Afirka na 2025 (AFCON) zai haifar da babban cikas a duk faɗin Gasar Premier, inda ake sa ran ‘yan wasa 40 na Afirka daga ƙungiyoyi 17 za su tafi gasar tsawon wata guda da aka tsara daga 21 ga Disamba 2025 zuwa 18 ga Janairu 2026 a Morocco, a wata rahoto da ta fito.
Ganin yadda gasar ke gudana a lokacin da ake sa ran kakar wasa ta Turai za ta kasance ba tare da manyan ‘yan wasa na farko ba har zuwa wasanni bakwai, ciki har da wasannin Premier League na Ingila da wasannin cin kofin gida.
Kasashe irin su Morocco, Masar, Afirka ta Kudu, Senegal, Najeriya da kuma zakarun da ke kare kambun Ivory Coast suna cikin manyan masu fafatawa don lashe gasar nahiyar.
Ƙungiyar Kwallon Kafar Wolves na fuskantar mafi girman koma baya saboda ‘yan wasan da zasu tafi don yin wasa wa ƙasashensu na haihuwa.
Ga cikakken jerin ‘yan wasan Premier League da ake sa ran za su shiga gasar AFCON 2025, kamar haka
Algeria
Rayan Aït-Nouri — Manchester City
Burkina Faso
Dango Ouattara — Brentford
Bertrand Traoré — Sunderland
Cameron
Carlos Baleba — Brighton
Bryan Mbeumo — Manchester United
Jackson Tchatchoua — Wolves
DR Congo
Axel Tuanzebe — Burnley
Arthur Masuaku — Sunderland
Noah Sadiki — Sunderland
Egypt
Mohamed Salah — Liverpool
Omar Marmoush — Manchester City
Ivory Coast
Evann Guessand — Aston Villa
Amad Diallo — Manchester United
Ibrahim Sangaré — Nottingham Forest
Willy Boly — Nottingham Forest
Simon Adingra — Sunderland
Emmanuel Agbadou — Wolves
Mali
Cheick Doucouré — Crystal Palace
Morocco
Amine Adli — Bournemouth
Chadi Riad — Crystal Palace
Adam Aznou — Everton
Noussair Mazraoui — Manchester United
Chemsdine Talbi — Sunderland
Mozambique
Reinildo Mandava — Sunderland
Nigeria
Frank Onyeka — Brentford
Christantus Uche — Crystal Palace
Alex Iwobi — Fulham
Calvin Bassey — Fulham
Samuel Chukwueze — Fulham
Tolu Arokodare — Wolves
Senegal
Ismaila Sarr — Crystal Palace
Iliman Ndiaye — Everton
Idrissa Gueye — Everton
Habib Diarra — Sunderland
Pape Matar Sarr — Tottenham
El Hadji Malick Diouf — West Ham
South Africa
Lyle Foster — Burnley
Tunisia
Hannibal Mejbri — Burnley
Zimbabwe
Marshall Munetsi — Wolves
Tawanda Chirewa — Wolves


