Tuhume-tuhumen cin zarafi yasa Molde FK ta dakatar da Daniel dan Najeriya.
Dan wasan tsakiya na kwallon kafa ta Najeriya mai tashe Daniel Daga, yana fuskantar shari’a bayan ana tuhume shi da laifin cin zarafin wa ta mata ba tare da izini ba a kasar Norway.
Kungiyarsa ta Molde FK, ta tabbatar da wannan lamari, wanda ya haifar da cece kuce a tsakanin ‘yan wasan Eliteserien da kuma ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya, a wata sanarwa da ta aka fitar a ranar Juma’a.
Matashin dan wasan mai shekaru 18, wanda kwanan nan ya koma buga kwallon kafa a Turai, an dakatar da shi daga dukkan ayyukan kungiyar, da suka hada da notsa jiki da wasannin gasa, yayin da ake ci gaba da shari’ar.
A cewar mai gabatar da kara, tuhume-tuhumen sun samo asali ne daga wani lamari da ya faru a lokacin kakar wasa ta farko a Norway.
Duk da cewar ba’a sanar da cikakken bayanin abun da ya faru ba, don kare bangarorin da abin ya shafa, Kotun Gundumar Nordmøre da Romsdal ta tsara zaman sauraren karar a watan Maris na 2026.
An ruwaito cewa dan wasan ya kasance mai bada hadin kai a duk lokacin binciken farko, yana halartar da amsa duk tambayoyin da ‘yan sanda suka yi masa.
Duk da cewa ya dawo Najeriya tun daga lokacin, ana sa ran zai koma Norway don fuskantar shari’ar a bazara mai zuwa.
Molde FK, ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyi ne a Norway, ta ɗauki mataki mai ƙarfi kan wannan lamarin.
Shugaban ƙungiyar Odd Ivar Moen ya jaddada muhimmancin tuhumar yayin da ya amince da wahalar da lamarin ke haifarwa ga duk masu ruwa da tsaki a ƙungiyar.
“Wannan lamari ne mai mahimmanci, kuma muna ɗaukar tuhumar da muhimmanci,” in ji Moen.
“Irin waɗannan shari’o’in suna da matuƙar wahala ga duk wanda abin ya shafa.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu yi aiki da gaskiya da kuma tabbatar da adalci da girmama dukkan ɓangarorin.
Ƙungiyar ta kuma ɗauki matakin tuntuɓar lauyoyin mai ƙara, tana mai amincewa da “nauyin na sirri” da shari’ar ta ɗora wa wanda abin ya shafa.
Duk da tuhumar da ake yi masa a hukumance, wadda ya ke wakiltar Daniel Daga a shara’ance ya tabbatar da cewa ba shi da laifi.
Lauyansa, Astrid Bolstad, ya tabbatar da cewa yayin faruwar lamarin jima’in ɗan wasan tsakiya ya tabbatar da cewa anyi shi bisa amince duk kanin su gaba ɗaya. Babu wata shaida ko zargin tashin hankali ko barazana da aka samu a lokacin
Daniel Daga ya je ƙungiyar ta Molde kafin kakar wasa ta 2025 a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan wasan tsakiya masu tasowa a Afirka.


