Amurka ta rattaba hannu kan sabbin yarjejeniyoyi guda hudu na kiwon lafiya da kasashen Madagascar, Saliyo, Botswana da kuma Habasha ko Ethiopia, wadanda zasu samar da kudade har dala miliyan dubu 2 da 300 na aiwatarwa.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fada cikin wata sanarwa ranar talatar nan cewa, kowace daya daga cikin yarjejeniyar ta tanadi irin ci gaban da ake son ganin an samu, da lokacin aiwatarwa, da kuma sakamakon da zai biyo bayan ki ko aiwatar da ita.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce makasudin hakan shine tabbatar da cewa hakar zata iya cimma ruwa a duk wani agajin da Amurka zata bayar wajen takalar cututtuka masu barazana tare da rage irin dogaro da kasashen keyi na dogon lokaci a kan agaji daga Amurka.
Ta ce karkashin wadannan yarjejeniyoyi da kasashen hudu, Amurka ta yi alkawarin bayar da kusan dala miliyan dubu 1 da 400, yayin da su kuma kasashen da zasu samu wannan agaji zasu zuba dala miliyan 900 daga aljihunsu.


