Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Da Ya Rutsa Da Antothy Joshua
Published: December 29, 2025 at 11:08 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Dan wasan dambe na kasar Birtaniya, Anthony Joshua ya yi hatsarin mota a jihar Ogun da ke Nigeria, hatsarin ya yi sanadiyar rayukan mutane biyu, a cewar ‘yan sanda ranar Litinin.

‘Yan sandan na jihar Ogun sun ce motar su Anthony Joshua ta yi karo ne da wata motar, kuma An kai shi asibiti, inda suka kara da cewa suna gudanar da bincike kan dalilin faruwar hatsarin.

Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta ce mutane biyar ne hatsarin ya rutsa da su a hanyar Lagos-zuwa Ibadan, inda Joshua ya samu raunuka kadan, mutum biyu suka mutu, wasu biyu kuma ba su samu rauni ko kadan ba.

Hukumar ta ce, farkon bincike ya nuna motar da take dauke da Mr. Joshua tana zura gudu ne sai kan motar ya kwace, yayin da take kokarin wuce wata mota, da tayi karo da wata gingimari da ke ajiye a gefen titi.

Anthony Joshua, wanda ya kasance iyayen sa ‘yan Nigeria ne da Birtaniya, ya yi makarantar kwana ne a garin Ikenne, wanda ya ke mil 53 daga inda hatsarin ya faru, kafin daga bisani ya koma Birtaniya yana da shekara 12.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan
Next Post: Kasar Amurka Tabada Tabbacin Bawa Ukraine Tsaron Shekarun 15

Karin Labarai Masu Alaka

Hawan Durba A Fadar Sarkin Zazzau Afrika
Masana Lafiya – Preeclampsia Cuta Ce Mai Hadari Amma Ana Iya Magance Ta Afrika
Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Man Fetur A Najeriya Afrika
Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike A Tituna Najeriya
Gwamnatin Najeriya Ta Tura Mutane 386 Gidan Yari Afrika
Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Nasarawa United Ta Kai Wasan Kusa da Ƙarshe Na Gasar Gusau/Ahlan 2026 Wasanni
  • Ministan Tsaron Najeriya Badaru Yayi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakoncin Wasannin Afirka Na 2031 Wasanni
  • Sojin Saman Najeriya Sunyi Gagarumar Nasara A Yankin Borno Najeriya
  • Malaman Tsangaya A Gombe Sun Goyi Bayan Inuwa Yahaya Da Jamilu Gwamna Afrika
  • Rahoton Leken Asiri Yanuna Cewa Harin Amurka Bazai Samar Da Shugabanci A Iran Ba Afrika
  • Tarayyar Turai Zasu Kirkiro Sojojin Haɗin Gwiwa Labarai
  • Shugaba Bola Tinubu Ya Amince Da Inganta Wutan Lantarki A Kasar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.