Amurka ta tallatawa Ukrain tabbacin samun tsaro na tsawon shekaru 15, a cikin kudurin ta na kawo zaman lafiya, a cewar shugaban Ukrain Vlodomyr Zelensky ranar Litinin, duk da dai ya ce shi ya fi son a ce an basu tabbacin tsaron na shekaru 50, don hana kasar Rasha kara yin wani yunkuri na kwace kasar makwabciyar ta da karfin tsiya.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya karbi bakunci Zelensky a wani wurin shakatawa a jihar Florida ranar Lahadi, kuma ya dage kan cewa Ukrain da Rasha suna gab da cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Amma masu tattaunawa a kan batun suna kan neman yadda za’a bullowa muhimman abubuwa, ciki har da dakarun wace kasa ce zasu janye, kuma daga in, da kuma makomar masana’antar nukiliya na Zaporizhzhia da Rasha ta mamaye, wanda yana daga cikin goma mafi girma a duniya.
Trump ya ankara cewa sasantawar da Amurka ke jagoranta wadda aka dauki wata ana yi da zata iya wargajewa.


