Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ), Comrade Alhassan Yahaya Abdullahi, ya bayya cewa, ƴan jarida da ke aiki a kafafen yaɗa labarai na gwamnati da masu zaman kansu na fama da rashin albashi mai kyau a Najeriya.
Comrade Yahaya, ya bayya hakan ne a hirarsa da Manema labarai ranar Juma’a, yana mai cewa akwai wani ƙudiri da za su gabatar da gaban Majalisar Tarayya.
Ya ce ƙudirin na da nufin inganta albashi da walwala da kuma yanayin aikin ƴan jarida, tare da magance matsalolin tauye ƴancin faɗin albarkacin baka a fadin ƙasar.
Ya kuma koka kan yadda mallakar kafafen yaɗa labarai ke komawa hannun ƴan siyasa mai makon ƴan jarida “masu ra’ayin tabbatar da gaskiya da kuma adalci.”


