Game da Hambarar da Mulkin Shugaban Kasar Venezuela Hukumomin duniya kuma, sunce “Wannnnan matakin ya kasance misali mai hadari, kan yadda za’a gudanar da al’amura nan gaba” inji kakakin sakataren MDD Antonio Gutierrez, ya ci gaba da cewa, sakataren na MDD yana jaddada muhimancin dukkan kasashen duniya su su mutunta dokokin kasa da kasa, ciki harda sharudda da dokokin MDD.
Mr. Gutierrez inji mai magana da yawunsa, yana nuna matukar damuwa cewa anan dai ba’a mutunta dokokin kasa da kasa ba.”
A nata bangaren Jamus ta bakin ma’aikatar harkokin wajen kasar tace, “Muna kira ga duk wadanda wannan lamari ya shafa, su gujewa ruruta wannan yanayi, kuma su nemi hanyoyin hannyoyin warware wannan batu ta fuskar siyasa,” Ta kara da cewa, Venezuela tana bukatar ko ta cancanci zaman lafiya, da tafarkin demokuradiyya nan gaba.”
China a nata bangaren, ma’aikatar harkokin wajen kasar tace, “Sin ta kadu, kuma tayi Allah wadai da kakkausar lafazi, amfani da karfin soja kan kasa mai ‘yanci, da kuma amfani da karfin soja kan shugaban kasa.”
Shi kuma da yake magana kan wannan lamari, ministan harkokin wajen Faransa yace, “matakin soja da ya kai ga kama shugaba Maduro, ya kaucewa amfani da karfi kamar yadda yake a dokokin kasa da kasa itama faransa ta sake jaddada cewa ba za’a samu zaman lafiya mai dorewa ba, idan aka tilasta shi daga ketare, Faransa tace ‘yan kasa ne kadai za su iya shata makomar su.
Da take magana kan wannan batu, ma’aikatar harkokin wajen Rasha tace, “A safiyar nan, Amurka ta nuna fin karfi ta amfani da karfin soja kan kasar Venezuela, wannan abun damuwa ne matuka, kuma abun Allah wadai ne.
Afirka ta kudu ta bakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bukaci kwamitin sulhu na MDD, yayi zaman gaggawa domin duba wannan lamari.
A kasashe dake Latin Amurka ra’ayoyi shugabannin kasashen sun sha ban ban, wasu suna Allah wadai da matakin, wasu kuma suna san barka.


