Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki
Published: November 17, 2025 at 6:34 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Da farko a karshen makon jiya ne babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta gudanar da taronta na kasa a birnin Badun, babban birnin jihar Oyo. inda ta zabi sabbbin shugabanni. Lauya Kabiru Tanimu Turaki, shine aka zaba sabon shugaban jam’iyyar. Aka kuma zabi Taofeek Arapaja, a matsayin sakataren jam’iyya. Babban taron ya kuma kori wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da Ministan raya birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike da wadansu, kan zargin suna yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Don samun haske akan wannan dambarwar, abokin aikin mu Yusuf Aliyu Harande ya tattauna da wani masanin siyasa kuma lauya mai zaman kanshi.

“Akwai bukatar jam’iyyu a Najeriya su dinga mutunta hukunce-hukuncen Kotuna, ba don komai ba kuwa sai don mutunta doka da oda daga mahukunta. Rashin mutunta hukuncin kotu da jam’iyar PDP ta yi zai iya jefa ta cikin mawuyacin hali.” A cewar Lauya Bala Usman, wani lauya mai zaman kanshi a Abuja.

Sau da yawa idan kaga ana takaddama, to abu da yafi kamata shine a garzaya kotu, don magance matsalar, kamar yadda Alh. Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, yayi na garzayawa kotu bayan hana shi sayen form da aka yi na tsayawa takarar shugabancin jam’iyar. Wani abu ne da zai iya haifar da babbar matsala a cikin jami’iyar a gaba.

Duk kuwa da cewar kotu ta bada umurnin kada a yi wannan taron, baya ga karar da Lamido ya shigar, wata kotu ta bada akasasin wannan hukunci, shi yasa wasu ‘yan jam’iyyar cigaba da gabatar da taron.

Barista Bala, yana kira da mahukunta da su dinga mutunta hukuncin kotu, da kuma yin amfani da matsayin su na siyasa don yin garon bawul ga bangaren shari’ar kasar, don gujewa irin wadannan matsalokin.

Yana kuma ganin wannan taron bashi da hurumin zaben wannan shugaban da suke ikirarin sun yi da kuma korar wasu ‘yan jam’iyar. Lallai babu shakka idan aka koma wajen wannan kotun zata soke wannan taron, da cire sabon shugaban jam’iyyar da aka zaba.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2025/11/Rikicin-Jamiyyar-PDP.mp3
Najeriya

Post navigation

Previous Post: Zelensky Na Ukraine Zai Gana Da Takwaransa Na Faransa A Yau
Next Post: An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya!

Karin Labarai Masu Alaka

Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA Afrika
Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa Labarai
Jihar Gombe Tayi Fice A Bangaren Inganta Lafiya Matakin Farko Najeriya
Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kotu Tayi Watsi Da Tarukan ADC Bangaren David Mark Afrika
  • CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • AFCON ChelIe, Ya Fidda Sunayen ‘Yan Wasan Super Eagles Na Karshe. Wasanni
  • Harin Jirgi Maras Matuki Ya Hallaka Mutane A Sudan Labarai
  • Thailand Da Cambodia Sun Fara Tattauunawa Kan Batun Tsagaita Wuta Labarai
  • Shugaba Trump Da Gwamnan Minnesota Zasu Sassautawa Bakin Haure Amurka
  • Ankara Kai Wani Harin Bom Birnin Maiduguri Afrika
  • Hukumar Tsaron Civil Defence A Gombe Ta Samar Da Jami’ai Don Tabbatar Da Tsaro A Bukukuwan Karshen Shekara Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.