Dama dai tun a watan Junairun shekarar da ta gabata ne tsohon ministan kuɗaɗen Ghana, Ken Ofori-Atta ya tsere daga Accra zuwa Amurka da sunan neman lafiya.
Tsohon ministan wanda gwamnatin Accra ta zarge shi da badaƙalar maƙudan kuɗaɗe, har ma ta ce ya tsere daga ƙasar ne saboda gudun fuskantar shari’a, ya nemi tsawaita zamansa a Washington a cewar lauyoyinsa.
To amma jami’an hukumar shige da fice na ƙasar sun kama shi, inda zuwa yanzu babu masaniya game da inda aka ajiye shi a cikin Amurkan.
Sanarwar da tawagar lauyoyinsa suka fitar, ta ce suna tatttaunawa da jami’an tsaron Washington don ganin an sake shi nan bada jimawa ba, a cewarsu shi ma tsohon ministan yana bai wa jami’an haɗin kai.
Ofori-Atta, dai ya kasance ministan kuɗi na Ghana tun daga shekarar 2017 har zuwa ta 2024, zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasar Nana Akufo-Addo, inda ya jagoranci aiwatar da sauye-sauye da dama a fannin tattalin arziƙin ƙasar, wanda gwamnatin John Dramani Mahama ke adawa da su.


