Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayin Shanu
Published: January 9, 2026 at 7:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe ta sanar da kama mutane hudu tare da kwato dabbobi masu yawa da ake zargin an sace su, a wani yunkuri na dakile satar dabbobi da fashin shanu a fadin jihar.

A cewar kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, samamen ya gudana ne da hadin gwiwar ’yan sa-kai da mafarauta.

A yayin ayyukan, an kama wasu matasa a yankunan Yamaltu-Deba, Kaltungo da Balanga, tare da kwato shanu biyu, tumaki 274, awaki 54 da jaki guda.

Rundunar ta ce an gano wasu daga cikin dabbobin nan take daga hannun masu su, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran masu dabbobin da kuma cafke wadanda ke tsere.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya yaba da hadin gwiwar al’umma, tare da jaddada kudirin rundunar na yakar satar dabbobi da sauran laifuka. Ya kuma bukaci jama’a da su rika bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro.

’Yan sanda sun tabbatar da cewa za a gurfanar da dukkan wadanda aka kama gaban kotu bayan kammala bincike.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Jihar Gombe Ta Haramta Sana’ar Bola Jari
Next Post: Fiye Da Mutane 10 Sun Mutu A Hatsarin Hanyar Kano

Karin Labarai Masu Alaka

Zamfara: Sai Mun Hada Kai Don Kawo Karshen Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Iran Ta Kama Wasu ‘Yan Leken Asiri Afrika
Janar Rabe Abubakar Ya Mutu A Tsare A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane Afrika
Sudan Takai Hari Kasar Chadi Da Jirgi Marar Matuki Afrika
Ukraine Da Syria Zasuyi Haɗin Gwiwar Tsaro Labarai
Meyasa Israela Take Hana Kaiwa Gaza Kayan Tallafi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • AFCON ChelIe, Ya Fidda Sunayen ‘Yan Wasan Super Eagles Na Karshe. Wasanni
  • Bayan Shekaru Biyar, Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Gano Motar da Aka Sace A Fatakwal Afrika
  • Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar Ya Shiga Jam’iyyar APC Siyasa
  • Jami’ai A Mexico Sun Tabbatar Da Kashe Shugaban Masu Shan Ƙwaya Nemesio Oseguera Labarai
  • An Kara Wa’adin Zaman Kurkuku A Senegal Ga Masu Auren Jinsi Afrika
  • Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Wani Kauye A Jihar Sakkwato Tsaro
  • CAN: Da Alamu Daliban St. Mery Na Cikin Koshin Lafiya Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.