Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Kungiyar Enyimba: Bamu Da Niyyar Rage Albashin ‘Yan-Wasa
Published: November 20, 2025 at 3:25 PM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: November 20, 2025

Kungiyar Kwallon Kafa ta Enyimba dake ABA a Najeriya ta fidda wata takarda wacce ta raba wa manema labarai. Takardar dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ƙungiyar SAMPSON ORJI.

Inda suke nisanta kansu da wani labari da ya ja hankali a shafin sada zumuntar zamani cewar ƙungiyar ta Enyimba FC. Ta rage Albashin ‘Yan Wasa da kashi 50% bayan shan kaye a gida a hannun Wikki Tourist FC. daci 1-0 cikin gasar firimiya lig na Najeriya mako na 13.

Kungiyar Enyimba FC tace babu wani lokaci da shugabanninta suka amince, suka fara, ko aiwatar da wani rage albashi, na yan wasanta ba.

“Wannan rahoton wani abu ne kawai na tunanin marubucin kuma ya kamata jama’a su yi watsi da shi.” inji Enyimba.

Kungiyar ta nuna damuwa cewa irin wannan labarin karya ya fito ne daga wata kafar yada labarai da ake kyautata zaton ba tare da wani yunkurin tabbatar da sahihanci daga kungiyar ko ta hanyar shugabanninta ko kafofin watsa labaranta ba.

Kungiyar Enyimba FC, na goyon bayan girmama juna da kafofin watsa labarai da suka dade suna yi, ta ci gaba da mayar da hankali kan komawa ga hanyoyin nasara.

“Za mu ci gaba da yin aiki kafada da kafada da abokan hulɗar kafofin watsa labarai, don haskaka ayyukanmu da kuma ba da gudummawa ga ci gaban NPFL da ci gaban ƙwallon ƙafa a Najeriya.”

Hukumar shirya gasar cin kofin (NNL) a Najeriya ta tabbatar da janyewar ƙungiyar kwallon kafa ta Dakkada FC da ke Uyo daga gasar NNL26 mai zuwa.

“Hukumar ta yi alƙawarin daidaita jadawalin wasannin domin samar da hanyoyin da za a bi wajen cimma burin da aka sa a gaba. Hakan ya zama dole saboda janyewar ƙungiyar DAKKADA FC daga gasar.” Inji Hukumar.

DAGA KASAR GHANA:

Wani mamba a hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Ghana (GFA) Frederick Acheampong, ya ziyarci magoya bayan kulub din Aduana FC da suka ji rauni a wani hatsari a kan hanyarsu ta dawowa gida, bayan wasan GPL da su kayi da ƙungiyar kwallon kafar Asante Kotoko a Kumasi.

Hatsarin da ya jawo harda rasa rayuka. Frederick ya mika ta’aziyya ga iyalai da duk masoyan magoya bayan biyu da suka rasa rayukansu a hatsarin.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2025/11/RAHOTON-WASANNI-DARE-19-11-2025.mp3
Wasanni

Post navigation

Previous Post: An Gudanar Da Taron Matasan Kasashe 6, Don Kawo Karshen Ta’addanci
Next Post: Madrid, Arsenal Da Chelsea Sun Fara Zaurancen Dan-Wasa Kenan Yildiz

Karin Labarai Masu Alaka

Abu Mafi Daukar Hankali A Wasan Dambe Na Yau Wasanni
Okoye Na Shirin Maye Gurbin Nwabali, AFCON 2025: Wasanni
Motsepe, Daga 2028 AFCON Zata Sauya Daga Shekaru Biyu Zuwa Hudu Wasanni
Kano Pillars Ta Doke Ikorodu City Wasanni
Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
Dangantaka Tayi Tsamari Tsakanin Salah Da Slot. Wasanni

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jam’iyar APC A Najeriya Ta Kaddamar Da Bada Shaidar Zama Dan Jam’iyyar Ta Na’ura Mai Kwakwalwa
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Umarci Janye ‘Yan Sanda Masu Gadin Ministoci Tsaro
  • Jirgin Sojojin Ruwa Yayi Gobara A Cross River Najeriya
  • Gwamna Ahmad Aliyu Na Jihar Sokoto Ya Gabatar Da Kasafin Fiye Da Naira Biliyan 700 Labarai
  • Somaliya: Ba Za Mu Dauki Wulakancin Donald Trump Ba! Sauran Duniya
  • Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
  • Kyaftin Na Super Eagles Ya Yi Ritaya. Wasanni
  • Hukumar EFCC Ta Kwace Gidan Tsohon Antoni Janar Abubakar Malami Najeriya
  • Alaka Na Cigaba Da Kamari Tsakanin Rwanda Da Barundi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.