Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Kyautata Dangantaka Tsakanin Jami’an Tsaro Da Al’umma Ce Mafita
Published: November 22, 2025 at 3:30 AM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: November 23, 2025

Masana harkokin tsaro a Najeriya sun bayyana cewa kyakkyawar alaka da fahinta tsakanin jami’an tsaro da al’umma, suna da gagarumin tasiri wajen magance matsalolin tsaro da samun zaman lafiya mai dorewa.
A wata tattaunawa ta musamman da sashen hulda tsakanin farar hula da jami’an soji da shelkwatar rundunar ta shirya da manema labarai a Jos, jihar Filato, masana harkokin tsaro, jami’an soji da ‘yan jarida sun dauki wuni guda suna fadakar da juna matakan da kowa zai bi wajen samadda masalaha kan matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya.
Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka mai ritaya, wanda ya gabatar da kasida mai taken “Tasirin Fasahar dake tasowa kan kafafen watsa labarai da hadin gwiwa tsakanin soji da kafafen watsa labarai”, ya bayyana cewa idan har ‘yan jarida sun fahinci yadda soja ke gudanar da aikinsu, suka kuma fadakar da al’umma, ba shakka za’a sami ci gaba.
Madam Ayuku Pwaspo, shugabar kungiyar ‘yan Jarida ta kasa reshen jihar Filato, ta bukaci manema labarai su gudanar da aikinsu bisa ka’ida don hadin kan kasa.
Shugaban sashen hulda tsakanin farar hula da soji, Manjo Janar Musa Etsu-Ndagi yace ‘yan jarida na da gagarumin gudunmawar fadakar da jama’a yadda soja ke aiki.
Hajiya Hadiza Hassan, ‘yar jarida dake aiki a gidan Rediyo da Talabijin na Unity a Jos, tace ta karu sosai daga tattaunawar.
Wassu faifan bidiyo da hotuna da rundunar sojin da nuna sun bayyana irin tallafi da sojoji ke baiwa al’umma da suka hada da gyara da gina makarantu da asibitoci, tallafin kayan abinci ga wadanda suka shiga ibtila’i da sauransu.
Najeriya

Post navigation

Previous Post: Manya-Manyan Wasannin Wannan Makon
Next Post: Tsananta Hukunci Ga Masu Fyade Kan Takaita Cin Zarafin Yara

Karin Labarai Masu Alaka

An Gabatar Da Sabbin Kudurorin Kare Muhalli Da Gandun Daji A Gombe Afrika
Gwamnatin Tarayya Tana Neman Kudi Domin Aiwatar Da Kasafin Kudin 2026 Najeriya
Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos Afrika
Dakaru Sun Hallaka ’Yan Ta’adda Masu Yawa – DHQ Afrika
Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000 Najeriya
Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar CAC Zata Dakatar da POS Mara Rijista a Kasar Najeriya
  • ‘Yan Ta’adda Sun Tarwatsa Wani Kauye A Jihar Sakkwato Tsaro
  • Gwamnatin Kasar Nijar Ta Kame Babban Dan Jarida Afrika
  • Kasar Amurka Da Denmark Suna Rikici Akan Iyakar Greenland Amurka
  • Gwamnan Jihar Filato Na Shirin Komawa APC Siyasa
  • Kudaden Shigan Kasar Namibia Ya Bunkasa Saboda Tashin Farashin Gwal Labarai
  • Kasar Masar Ta Dakatar Da Wasu Ayyukan Da Ake Amfani Da Man Fetur Da Diesel Labarai
  • Shirin Kwace Iyakar Greenland Da Shugaba Trump Yakeyi Yabawa Kasashen Turai Mamaki Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.