Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Hukumomin Tsaron Kenya Sunce ‘Yan Kasar Suna Fafata Yaki Da Dakarun Rasha A Ukraine
Published: February 20, 2026 at 1:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rahotanni daga hukumomin tsaro a Kenya sunce fiye da ‘yan kasar dubu daya ne aka dauka domin yaki da dakarun Rasha a Ukraine, kamar yadda bayanai da hukumomin tsaron kasar suka gabatarwa wakilan majalisar dokokin kasar a makon nan, wannan adadi ya ninka sau biyar kan kiyasin farko da hukumomin kasar suka yi.

Sai dai ofishin jakadancin Rasha a Nairobi ranar Alhamis ta musanta cewa Rasha tana da hanu wajen daukar ‘yan kasar Kenya ba bisa ka’ida ba domin su taimake ta da yaki a Ukraine, amma tace ‘yan kasashen ketare domin radin kansu suna iya shiga rundunar sojan kasar.

Da yake karanta rahoton ga wakilan majalisar, shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin kasar, ya zargi wasu baragurbin ma’aikatan gwamnati da suke hada baki da miyagun kungiyoyi masu safrar mutane wajen daukar ‘yan kasar kenya domin shiga yaki a ukraine a amadadin Rasha.

Masu daukar su aikin suna auna tsoffin sojoji da ‘Yan sanda, da kuma marasa ayyukan yi, tare da yi musu alkawarin za a biya su dala dubu biyu da dari bakwai da 15 a ko wani wata sannan za’a ba su dala dubu tara da dari uku da tara a zaman tukuici.

Zuwa wannan wata na Faburairun , yanzu haka akwai ‘yan kasar Kenya 89 a fagen daga a Ukraine, 39 suna asibiti, yayinda wasu 28 sun bace a fagen yaki ba’a sn inda suke ba.

Afrika, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kasashe Biyar Zasu Tura Sojoji Domin Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Gaza
Next Post: Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa Afrika
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ta Saka Takunkumi Visa Ga Wasu ‘Yan Rwanda Afrika
CNG Ta Farfado Da Jarin Masu Adaidaita Sahu A Kaduna Afrika
Yayale Ahmed Ya Jagoranci Kwamitin Amintattu Na Asusun Tsaron Arewa Afrika
Burkina Faso: Mun Kama Sojojin Najeriya da Jirgin Yaki Bisa Shigowa Ba Bisa Ka’ida Ba Afrika
An Sace Masu Ibada A Wata Majami’ar Ecwa A Jihar Kogi Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
  • Janar Rabe Abubakar Ya Mutu A Tsare A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane Afrika
  • Kwankwaso Yayi Kakkausar Lafazi Bayan Ficewar Abba Kabir Yusuf Daga NNPP Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka
  • Ba Shakka Najeriya Zata Iya Shiga Gasar Harbi Ta Duniya Wasanni
  • Majalisar Tarayya Ta Amince Da Mutane Uku A Matsayin Jakadun Kasashen Waje Labarai
  • Shugaban Hukumar NAHCON Ya Ajeye Mukaminsa Labarai
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwar da Mutane a Jihar Gombe Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.