Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaban Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka A Afirka Yace Akwai Rashin Fahimta A Tsakanin Kasashen Da Amurka Take Tallafawa
Published: February 27, 2026 at 4:43 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Akwai manyan batutuwa ko rashin fahimta dake kunno kai a yarjejeniyar kiwon lafiya da Amurka take kullawa da kasashen Afirka dangane da yadda tallafin kudi da Amurka take bayarwa zai rika aiki daga yanzu, kamar yadda shugaban hukumar sa ido da hana yaduwar cututtuka a Afirka ya fada ranar Alhamis.

“Akwai damuwa sosai game da musayar bayanai dana cututtuka, inji darekta janar na hukumar Jean Kesaya ya fadawa taron manema labarai ta hanyoyin sadarwa na zamani.

Ranar Laraba, Zimbabwe ta janye daga shawarwari da Amurka kan tallafin kudi dala milyan 367 cikin shekaru biyar masu zuwa, ta nuna damuwa kan musayar muhimman bayanai, tana mai cewa yarjejeniyar babu adalci. Zambia ma tace ta nuna rashin gamsuwarta da tsarin.

Wasu masu raji kan kiwon lafiya sun soki tsari da ya bukaci kasashe ba-da-wani-bata-lokaci ba, su sanarda Washington idan aka sami bullar wata cuta mai yaduwa a zaman sharadin bada tallafin. Yarjejeniyoyin basu bada tabbacin idan aka hada maganin da zai shawo kan cuta ko cututtukan za’a raba da kasashen da cutuutkan suka bullo ba.

Ahalinda ake ciki kuma, a cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da Amurka da jamhuriyar demokuradiyyar kwango suka sanyawa hanu ranar Alhamis, ta nuna kasashen biyu sun amince da yarjejeniyar aiki ta fuskar kiwon lafiya kan kudi dala bilyan daya da milyan dari biyu, cikin shekaru biyar masu zuwa.

Yarjejeniyar zata maida hankali kan yaki da cutar dake karya garkuwar jiki, da ake yi wa lakabin HIV/AIDS da turanci, da cutar Malaria, da kuma kula da lafiyar iyaye mata masu juna biyu da jarirai, yaki da cutar shan inno ko polio, da kuma sa ido kan pullar cututtuka masu yaduwa, kamar yadda sanarwar ta fada.

Afrika, Amurka, Kimiya, Labarai

Post navigation

Previous Post: Gwamnan Jihar Adamawa Fintiri Ya Koma APC
Next Post: Amurka Zata Tantance Fararen Fata ‘Yan Afirka Ta Kudu

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
Gwamnatin Kasar Nijar Ta Kame Babban Dan Jarida Afrika
Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
Muna Kira Ga Kasashen Duniya Su Sa Baki Don A Saki Mohamed Bazoum Afrika
Kasar Afirka Ta Kudu Ta Tsare Wasu Amurkawa Amurka
An Maka Wasu Jami’an Immigration A Kotu Bisa Zargin Rashin Da’a A Birtaniya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Mbappé Ya Yi Hat-Trick Yayin Da Real Madrid Ta Lallasa Real Sociedad 4 Da 1 Wasanni
  • Na Duke Tsohon Ciniki Shirye-Shirye
  • Rasha Na Cigaba Da Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Ga Ukrain Labarai
  • Amurka Zata Bada Gudunwa Ga Masu Zanga-Zanga A Iran Sauran Duniya
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
  • Kasar Belarus Zata Taffawa Jamhuriyar Nijar Afrika
  • Alejandro Balde Na Dab Da Komawa Manchester United Daga Barcelona Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.