Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
  • Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Sama Da Zawiyya 100 Ne Suka Samu Tallafin Kayan Abinci Daga Al’mustapha Haji Sufi
Published: March 5, 2026 at 5:23 PM | By: Bala Hassan | Updated: March 5, 2026

A ci gaba da tallafawa wa al’umar musulmai a fadin duniya don su samu saukin rayuwa musamman wannan lokaci na watan Ramadan wata mai alfarma watan da ake neman falalar Ubangiji.

Alh Al’mustapha Haji Sufi Hasken Matasan Arewa da ke jihar Bauchi Arewa maso gabas a Najeriya ya taimaka wa Zawiya da Marayu da kuma marasa galihu da abunda zasu samu su ci a lokacin boda baki.

Sama da Zawiya 100 ne suka amfana da Shinkafa, Taliya Mangya, da dai sauran kayayyaki da kuma kudade a ka raba a wajan.

An raba shinkafa mai nauyin kilogram 50 da kuma kilogram 25, guda 200, da kuma mangyada Katon Tamanin da Katon din Taliya 100 tare da kimanin kudi sama da miliyon daya ne aka raba a wajan.

A yayin jawabinsa Al’mustapha yace Al’mustapha Haji Sufi yace wannan gudumawa ya fito ne ta hannuna hukumar raya Arewa maso gabas NEDC ta re da Kwamishinan Kudi na Jihar Bauchi Hon Yakubu Adamu PhD.

babban dalilinsa na irin wannan taimako shine ganin irin halin da al’umma suke cikin halin mawuyacin rayuwa a yanzu haka, kuma ni Mutumne da aduk lokacin da na samu alheri daga wani waje na kanso ace nima na taimaka wa na kasa dani dai dai gwargwadon abunda zan iya kuma gashi lokacin wata mai Albarka na Ramadan.’

Babban bako a wajan Alh Nasiru Musa Sudani ya yaba da kokari irin wadda Alh Al’mustapha Haji Sufi Hasken Matasan Arewa inda yace ba wannane na farko da ya fara ba sama da shekaru goma yana yin aikin alheri wa al’uma.”

Yace  saboda irin wannan abun alheri da Al’mustapha ya ke shi yasaea kulllum al’uma ki masa fatan alheri a rayuwar sa, ya kuma masa fatan alheri a dukkanin rayuwar sa.

Cikin wayanda suka samu wannan tallafi harda masu bukata ta musamman da kuma al’umar da suke gidan gyara hali da tarbiya na Bauchi.

Wasu daga cikin wayanda suka amfana da wannan tallafi sukace zasuyi amfani da wannan tallafi wajan Shan Ruwa a wannan wata mai alfarma kuma zasu sanya shi cikin addu’oin su a wannan watan Ramadan.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Wata Kotu A Abuja Ta Wanke Abba Kyari
Next Post: Shugaba Donald Trump Ya Bayyana Cewa Yana Cikin Masu Zaben Sabon Jagoran Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Jami’an Askarawa A Zamfara Sun Kama Na’urorin Fashewa Da Makudan Kuɗaɗe Afrika
‘Yan Jarida Sunyi Mummunan Hatsari A Bauchi Labarai
Fiye Da Mutane 108 Sun Rasa Rayukansu A Ambaliyar Kenya Afrika
Mutane 13 Sun Mutu Inda Wasu 57 Suka Jikkata A Barundi Afrika
Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800 Labarai
Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Wutan Lantarki A Jami’ar Bayero
  • Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa
  • Gwamnatin Najeriya Zata Rabawa Al’umma Tallafin Noma
  • Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kungiyar Kwadago Ta Shirya Zanga-Zanga A Najeriya Najeriya
  • An Fara Azumin Watan Ramadan A Najeriya Da Sassan Duniya  Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Mulkin Soja A Mali Ya Kirkiro Mukami Kamar Minista Afrika
  • Ministan Harkokin Wajen Rasha Dana Iran Sun Tattauna Don Kawo Karshen Yaki A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Nnamdi Kanu Ya Nemi A Mayar Da Shi Abuja Daga Gidan Yarin Sokoto Labarai
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
  • Gwamna Fubara: Rashin Kariya daga PDP Ne Ya Tilasta Ni Komawa APC Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.