Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Ukraine Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Tsarin Cimma Yarjejeniya
Published: November 26, 2025 at 3:55 PM | By: Nafisa Ahmad

A yau talata Ukraine ta bayyana goyon bayanta ga tsarin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da kasar Rasha, amma ta ce tilas sai an warware wasu muhimman batutuwan da suke kumshe cikin shirin a tattaunawa tsakanin shugaba Volodymyr Zelensky da shugaba Donald Trump na Amurka.

Wannan sako daga bitnin Kiev  na nuni da cewa matsin diflomasiyyar da Amurka take yi ya fara janyo abubuwa na alkhairi, amma kuma duk wani dokin da ake da shi game da cimma zaman lafiyar na iya kasancewa na dan karamin lokaci, domin kuwa Rasha ta ce ba zata yarda duk wani matakin da za a yarda a kai yayi nesa sosai da bukatunta ba.

Mashawarta na Amurka da na Ukraine sun tattauna a kan shirin zaman lafiya na baya bayan nan da Amurka ta gabatar ranar lahadi a Geneva. Sannan a jiya litinin da kuma yau talata, sakataren rundunar sojan kasa ta Amurka, Dan Driscoll, ya gana da jami’an Rasha a Abu Dhabi.

Jami’an Amurka da na Ukraine suna kokarin rage abubuwan da ake da sabanin ra’ayi a kansu a game da shirin Amurka na kawo karshen yaki mafi muni da aka gani a nahiyar Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Tsohon Shugaban Brazil Bolsanaro Zai Tafi Gidan Yari
Next Post: Amurka Ta Gabatarwa Sassan Dake Yakar Juna A Sudan da Shirin Tsagaita Wuta

Karin Labarai Masu Alaka

Ana Jimamin Mutuwar Giwa Mai Shekaru Kusan 60 A Kasar Kenya Sauran Duniya
Somaliya: Ba Za Mu Dauki Wulakancin Donald Trump Ba! Sauran Duniya
Amurka Zata Bada Gudunwa Ga Masu Zanga-Zanga A Iran Sauran Duniya
Asusun IMF Zai Bawa Kasar Misra Lamunin Sama Da Dala Biliyan 2 Sauran Duniya
Iran Ta Tasa Keyar Wani Jirgi Shake Da Mai Sauran Duniya
Gobara Mafi Muni Cikin Shekaru 60 A Hong Kong Ta Hallaka Rayuka Sauran Duniya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ana Gudanar Da Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnati A Kasar Tunisiya Siyasa
  • Kano Pillars Ta Doke Ikorodu City Wasanni
  • Amurka Ta Kama Wani Jirgin Dakon Mai Amurka
  • Shugaban Amurka Donald Trump Yace Bai Taba Shiga Jirgin Jeffrey Epstein Ba Labarai
  • Yanayin Sanyi Yayi Kamari a Yankin Gaza Tsaro
  • ‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha Afrika
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakoncin Wasannin Afirka Na 2031 Wasanni
  • Hukumar NAPTIP Ta Kubutar Da Yara 11 Daga Hannun Masu Safara Mutane Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.