Kasar Masar zata dakata da wasu manyan ayyukan raya kasa da ke bukatar amfanin da man fetur da na diesel me yawa a kalla zuwa watanni biyu, sannan za’a yanke adadadin man da ake bawa motocin gwamnati da kashi 30 cikin 100, a dalilin yakin da Amurka da Isra’ila ke tafkawa da Iran a cewar prime minista Mostafa Madbouly a ranar Asabar.
Madbouly ya kara da cewa dukkanin ma’aikatu dana gwamnati da masu zaman kan su, ban da ma’aikatun kere-kere, zasu rika gudanar da ayyukan su a gida ranar kowacce Lahadi a watan Afrilu. Za’a iya kara ranaku a cikin mako da za’a yi aiki a gida zuwa 2, ko kuma a kara wa’adin da za’a ci gaba da wannan tsari zuwa watanni na gaba idan yaki ya ci gaba da Gudana.
Wannan tsari na daga cikin matakan da ake dauka don fuskantar hauhawar farashin man fetur da sauran nau’in makamashi da Masar ke fama da shi tun bayan da Amurka da Isra’ila suka far wa Iran da yaki.


