Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan-Ta’adda Sun Kara Sace Mutane A Jihar Naija!
Published: November 27, 2025 at 1:44 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

A yayinda ake ci gaba da jimami da kuma neman yadda za’a samu kubutar da sauran Daliban Makarantar St. Mary a jihar Nejan Najeriya da ‘yan bindiga suka kwashe a Makon jiya.
Yanzu haka kuma wasu ‘yan fashin Dajin sun kai wani sabon hari a yankin Shiroro tare da yin awon gaba da wasu Mutane.
Dama dai yankin na Shiroro mai madatsar ruwan dake da daya daga cikin tashoshin dake samar da hasken lantarki a Najeriya ya dade yana fama da matsalar hare haren ‘yan bindigar.
Wani mazaunin yankin karamar Hukumar Shiroron da ya bukaci a sakaya sunanshi yace maharan sun shiga kauyen Unguwar kawo ne a ranar Laraban nan su kayi awon gaba da  mutane takwas, uku daga cikinsu mata ne da kuma karamin yaro guda.
Rundunar ‘yansanda ta Jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar lamarin sai dai tace bata gama tantance abinda ya faruba, kakakin yandan Wasiu Abiodun yace ya zuwa lokacin da muka tuntube shi basu fayyace abinda ya faruba.
Yace yaji batun harin amma zai kara bincikawa domin ba zai iya baka ainahin yawan mutanen da aka sacenba.
Bincike dai ya nuna a yanzu haka akwai garuruwa da dama a yankin Arewacin Jihar Nejan da kuma Arewa maso gabas da suka koma kufai saboda ‘yanbindigar sun fatattaki jama’a daga garuruwan.
Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Sojojin Da Suka Kifar Da Farar Hula A Guinea-Bissau Sun Sanar Da Cewa!
Next Post: Liverpool Tayi Rashin Nasara A Wasanni Tara

Karin Labarai Masu Alaka

Alhinin Rasuwar Bello Sharada, Fitaccen Mai Sharhi Kan Siyasar Najeriya Afrika
Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika
Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz Afrika
Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Bayan Rikicin Manoma Da Makiyaya, Kwamitin White Paper Ya Ziyarci Bojude Da Kwami Afrika
Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Arsenal Ta Doke Manchester City 3-0, Ta Ɗauki Kofin Community Shield Wasanni
  • Kasar Amurka Da Rasha Zasu Kawo Karshen Tsagaita Nukiliya Amurka
  • Zamu Tarwatsa Cibiyoyin Makamashi Da Cibiyoyin Mai Din Iran Amurka
  • Amurka Ta Sanya Hanu Kan Yarjejeniyar Kiwon Lafiya Da Ƙasashen Madagascar, Saliyo, Botswana, Ethiopia Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Tada Kayar Baya Sun Tayar Da Bom A Maiduguri Labarai
  • Sanyin Hunturu Yayi Ajalin ‘Yan Cirani A Morocco Afrika
  • Magoya Bayan Nice Sun Kai Hari Wa ‘Yan Wasansu Wasanni
  • Ghana Ta Haramta Hakar Ma’adinai A Gandunan Dajin Data Kebe, Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.