Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Netanyahu Yana Neman Shawarwari Daga Hukumomin Lebanon
Published: April 10, 2026 at 5:23 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Prime Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada jiya Alhamis cewa, yana neman shawarwari kai tsaye da hukumomin Lebanon a Beiruit, kwana daya bayan da Isra’ila ta kai hari mafi muni da bama-bamai tun fara yakin, har ta halaka mutane dari uku, wanda ya jefa yarjejeniyar tsagaita wuta da shugaba Donald Trump ya kulla da Iran, cikin hadari.

Wani jami’in Lebanon ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, ita ma Lebanon tana bukatar ta gudanar da shawarwari kai tsaye da Isra’ila na neman a tsagaita wuta, shigen abunda yake gudana tsakanin Iran da Amurka.

Trump ya bayyana shirin tsagaita wuta a yakin hadin guiwar Amurka da Isra’ila kan Iran da ya shiga mako shida, a daren talata, jim kadan kamin wa’adin da ya bayar ya kure, wanda yayi barazanar zai shafe Iran daga doron kasa.

A Pakistan, hukumomin kasar suna shirye shiryen zaman farko na shawarwari tsakanin Amurka da Iran, tuni har ta rufe wasu hanyoyi a Isalamabad babban birnin kasar.

Sai dai babu wata alamar cewa Iran ta bude mashigin ruwan Hormuz, matakin da ya janyo mummunar kassara jigilar makamashi a tarihi, inda Tehran take nuni da ci gaban hare hare da isra’ila take kai wa a Lebanon , a zaman dalili.

A cikin sa’o’i 24 tun bayan sanarda tsagaita wuta, jirgin ruwa mai dakon daya ne kadai, tare da wasu jirage masu dakon kaya 5 ne suka ratsa ta mashigin ruwa na Hormuz, hanyar da galibi jiragen ruwa 140 suke bi ako wace rana, inda ta nan ne kashi 20 cikin dari na makamashi da duniya ta dogara akai yake bi.

Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Sakataren Kungiyar NATO Yayi Magana Da Hukumomin Kasashe
Next Post: Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa

Karin Labarai Masu Alaka

Jami’yar ADC A Najeriya Ta Kori Nafiu Bala Afrika
Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa Afrika
An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
Sojin Kasar Congo Da ‘Yan Tawaye Sun Kara Shiga Yankin Uvira Labarai
Bahrain Ta Gabatar Da Kudurin Sulhu Ga MDD Afrika
Taron Sulhu Tsakanin Addinai Mabanbanta Na Arewacin Najeriya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Magoya Bayan Dan Hamayya A Afirka Ta Kudu Sun Hallara A Kotu Afrika
  • Motsepe, Daga 2028 AFCON Zata Sauya Daga Shekaru Biyu Zuwa Hudu Wasanni
  • Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
  • Nigeria Zata Bude Asusun Dala Bilyan Biyu Don Habaka Sashin Makamashi Labarai
  • Wasu Mayakan ‘Yan Tawaye Sunkai Hari Filin Jirgin Saman Kasar Kwango Labarai
  • Jami’yar ADC A Najeriya Ta Kori Nafiu Bala Afrika
  • Sunayen Jakadu: Kungiyar CISLAC Ta Nemi A Janye Sunan Mr. Ayodele Oke Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Tinubu Ya Turawa Majalisa Sunayen Mutane Biyun Da Zasu Shugabanci Sashin Albarkatun Mai Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.