Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Najeriya Zata Rabawa Al’umma Tallafin Noma
Published: April 18, 2026 at 4:13 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana aniyar ta na ganin cewa tallafin dala miliyan 500 da Bankin Duniya ya amince da shi, ya isa hannun manoma na hakika a fadin kasar nan, maimakon karkata shi ga akwakun ‘yan siyasa.

Shugaban Hukumar Ba da Tallafin Kuɗaɗen Haɗin Gwiwa na Ƙasa (NFC), Emmanuel Atama, shi ne ya tabbatar da hakan yayin wata hira da aka yi da shi kwanan nan. Atama ya bayyana cewa shirin an tsara shi ne don ya amfani akalla manoma miliyan daya, tare da magance matsalolin da suka dabaibayi shirye-shiryen da suka gabata.

Atama ya bayyana cewa daya daga cikin manyan matsalolin da suka hana tallafin noma tasiri a baya shi ne tsoma bakin siyasa da kuma rashin sahihan bayanai.

“Yawancin shirye-shiryen da aka yi a baya sun fuskanci cikas sakamakon rashin isasshen bayani ga manoma da kuma tsoma bakin yan siyasa, wanda hakan ya hana kuɗaɗen isa ga waɗanda aka yi niyya,” in ji shi.

Ya kara da cewa wannan karon tsarin zai bambanta, musamman sakamakon hadin gwiwa da Ministan Noma mai kwazo, wanda ya nuna shirye-shiryen cire duk wata sarkakiya da ke kawo cikas wajen aiwatar da ayyukan hukumar.

Shugaban ya kuma bayyana cewa tattaunawar da suka yi da Bankin Duniya ta bankado kurakuran da aka tafi da su a shirye-shirye irin su Anchor Borrowers Program. Saboda haka, wannan sabon tsarin zai mayar da hankali ne wajen gyara wadannan kura-kurai.

A halin yanzu, hukumar ta riga ta fara zagaye domin wayar da kan manoma a jihohi daban-daban, inda ake karfafa musu gwiwa su shiga kungiyoyin hadin gwiwa (cooperatives).

Wannan shi ne zai ba da damar tantance su cikin sauki da kuma tabbatar da gaskiya wajen rabon tallafin.

Wani sabon salo da shirin zai zo da shi don toshe kofofin almundahana shi ne raba kayan aikin noma maimakon kudi tsantsa. Atama ya fayyace cewa, Za a fi mayar da hankali wajen samar da takin zamani, iri, da injinan noma. Idan har akwai buƙatar bayar da kudi kai tsaye, ba zai wuce kashi 10% zuwa 15% na jimillar tallafin da manomin zai samu ba.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen hauhawar farashin abinci, inda ake fatan wannan tallafi zai bunkasa samar da abinci a fadin Najeriya.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz
Next Post: Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamna Abba Kabir Ya Zabi Garo A Matsayin Mataimaki Afrika
Jami’yar ADC A Najeriya Ta Kori Nafiu Bala Afrika
Da Arzikin Mu: Bamu Ba Bautawa Turawan Yamma Afrika
Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta Afrika
Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa Afrika
Za’a Gurfanar Da Sojojin Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu Afrika
  • Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Ta Bukaci Rwanda Ta Daina Marawa ‘Yan Tawayen M23 Baya Afrika
  • ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
  • EFCC Ta Cafke Fitacciyar Jarumar Kannywood Samha Inuwa Labarai
  • Rasuwar Tsohon Shugaban NUJ FCT, Osambedwan, Babban Rashi Ne — Ferfesa Alkali Afrika
  • Tsohon Alkalin Alkalai A Najeriya Ya Rasu Yana Da Shekaru 71 Labarai
  • Peter Obi Ya Gayyaci Gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Kan Yazo Su Hada Kai Su Gyara Nijeriya. Labarai
  • Kasar Saudiya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.