Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya
Published: May 25, 2026 at 12:38 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

NAHCON Ta Bukaci Mahajjata Su Sayi Dabbobin Hadaya Ta Cibiyoyin Da Aka Amince Da Su Kadai

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta yi kira ga dukkan maniyyatan Najeriya da ke gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 da su tabbatar sun sayi dabbobin Hadaya kadai ta hanyar dandalin Nusuk Masar ko kuma cibiyoyin sayarwa da Hukumar Kula da Ayyukan Hadaya da Adahi ta Masarautar Saudiyya ta amince da su.

Hukumar ta jaddada cewa bai kamata mahajjata su yi hulɗa da mutane ko ƙungiyoyi da ba su da izini ba wajen saye, talla, ko gudanar da duk wani aiki da ya shafi Hadaya da Adahi.

NAHCON ta bayyana cewa wannan mataki an ɗauke shi ne domin kare mahajjata daga zamba, damfara da sauran hanyoyin cutarwa, tare da tabbatar da cewa an kiyaye haƙƙoƙinsu a lokacin gudanar da ibadun Hajji.

Hukumar ta kuma bukaci mahajjata su yi amfani da hanyoyin da aka amince da su kawai domin tabbatar da cewa an gudanar da ibadar Hadaya da Adahi yadda Shari’ar Musulunci ta tanada tare da bin dokoki da ƙa’idojin Masarautar Saudiyya.

Hakazalika, an umarci Hukumomi da Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, Hukumomin Hajji da Umrah, Kwamitocin Alhazai da kuma Kamfanonin Shirya Hajji (Tour Operators) da su wayar da kan mahajjata tare da tabbatar da cikakken bin wannan umarni.

NAHCON ta yi addu’ar Allah Ya karɓi ibadun mahajjata baki ɗaya, Ya ba su Hajji Mabrur, Ya kuma dawo da su gida lafiya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11
Next Post: Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya

Karin Labarai Masu Alaka

Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
Aliko Dangote: Faruk Ahmed Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
Nnamdi Kanu Ya Nemi A Mayar Da Shi Abuja Daga Gidan Yarin Sokoto Labarai
Rasha Ta Yiwa Amurka Tayin Daina Bada Bayanan Sirri Afrika
Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Iran Ta Harbo Jiragen Yakin Amurka Biyu Amurka
  • Kamfanonin Jiragen Sama Suna Fama Da Karin Farashin Mai Labarai
  • Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka
  • ‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha Afrika
  • Jam’iyar SDP Tana Gudanar Da Babban Taro A Bauchi Afrika
  • Shugaba Trump Ya Bukaci A Cigaba Da Zanga Zanga A Iran Labarai
  • Magoya Bayan Nice Sun Kai Hari Wa ‘Yan Wasansu Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.