Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika

Kotu A Abuja Tabawa Goodluck Jonathan Daman Tsayawa Takara
Published: May 26, 2026 at 11:03 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wata babbar kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta yanke hukunci cewa tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya cancanci kuma zai iya tsayawa takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Kotun, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Peter Lifu na Babbae Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayyana hukuncin ne a ranar Talata, inda ta tabbatar da cewa babu wani tanadi na doka da ya hana Jonathan sake tsayawa takara.

Wannan hukunci ya biyo bayan shari’ar da wani mai shigar da ƙara, Johnmary Jideobi, ya shigar, yana neman kotu ta hana Jonathan tsayawa takara ko kuma bayyana kansa a matsayin ɗan takara a kowane jam’iyya a zaɓen 2027.

A cikin ƙarar, mai shigar da ƙara ya kuma nemi kotu ta hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, Independent National Electoral Commission, karɓa, sarrafawa ko bayyana sunan Jonathan a matsayin ɗan takara.

Sai dai mai shari’a Peter Lifu ya yi watsi da waɗannan buƙatu, inda ya bayyana cewa Jonathan na da cikakken haƙƙi a ƙarƙashin kundin tsarin mulki na 1999 da aka gyara, domin shiga takarar shugaban ƙasa.

Hukuncin kotun ya kuma zo ne a daidai lokacin da wani ɓangare na jam’iyyar PDP, ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, ya bayar da rangwame (waiver) ga Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Jonathan, wanda ya mulki Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015, ya sha kaye a zaɓen 2015 a hannun Muhammadu Buhari, lamarin da ya zama tarihi a siyasar ƙasar saboda shi ne shugaban ƙasa na farko da ya amince da shan kaye a zaɓen sake tsayawa mulki.

Hukuncin kotun na zuwa ne a matsayin wani muhimmin sauyi da ka iya ƙara ƙaimi a tseren siyasar 2027 da ake tunkara.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya
Next Post: Ferfesa Pantami Yasamu Tikitin Takarar Gwamnan Gombe A Jami’yar PDP

Karin Labarai Masu Alaka

Hawan Durba A Fadar Sarkin Zazzau Afrika
Fargaba Ta Karu Duk Da Tsagaita Wuta Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
Kasar China Ta Kaddamar Da Rawar Daji A Yankin Taiwan Labarai
Rahoton MDD Yace An Kashe Fiye Da Farar 1000 A Sudan Labarai
Amurka Da Isra’ila Sunkai Hari Kan Iran Amurka
Ruwan Sama Yayi Ajalin Daruruwan Mutane A Afirka Ta Kudu Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Kama Akalla Mutane 13 A Wani Coci A Jihar Kogi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Yayi Ajalin ‘Yan Ghana 50 Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Alhamis 11.20.2025 Rediyo
  • Sanata Sa’idu Alkali Ya Kaurace Wa Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Rundunar Hadinkan Saudiya Tayi Ikirarin Mayar Da Martani Ga ‘Yan Aware Labarai
  • Amurka Da Iran Zasu Tattauna A Kasar Oman Amurka
  • Sarkin Musulmi Yayi Magana Game Da Matsalar Tsaron Kasar Tsaro
  • Kasashen Amurka Da China Sun Matsawa Ghana Domin Rage Kudaden Haraji Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.