Shugabannin Kungiyar Kiristoci a Arewacin Najeriya sun miƙa saƙonnin taya murna ga Musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya, bisa shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci (Hijira 1448), inda suka jaddada muhimmancin zaman lafiya, jituwa da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.
Sun kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi la’akari da ayyana ranar Sabuwar Shekarar Musulunci a matsayin ranar hutu ta ƙasa, domin bai wa Musulmi damar gudanar da bukukuwan su cikin natsuwa da tunani.
Shugaban Majami’ar Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Kaduna, Pastor Yohanna Buru, ya taya Musulmi murna, tare da kiran a ƙara yin addu’o’in zaman lafiya da haɗin kai a Najeriya da yankin Yammacin Afirka baki ɗaya.
A yayin ziyararsa ga wasu malaman Musulunci, Pasto Buru ya ce wannan na daga cikin ƙoƙarinsa na ƙarfafa dangantakar addinai da inganta zaman lafiya tsakanin Kirista da Musulmi a jihar Kaduna da ƙasar baki ɗaya.
Ya ce ya saba amfani da kafafen sada zumunta wajen aika saƙonnin zaman lafiya a duk Sabuwar Shekarar Musulunci, domin taya abokansa Musulmi murna tare da yi musu fatan alheri.
Ya kuma buƙaci al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da zama cikin zaman lafiya, tare da goyon bayan matakan gwamnati na ƙarfafa haɗin kai da daidaito a ƙasa.
“Nigeriyawa su riƙa nuna haƙuri da yafiya, su kuma mara wa gwamnati baya wajen ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai na ƙasa da magance matsalolin da suka shafi ƙabilanci, siyasa da addini,” in ji shi.
A nasa jawabin, Pasto John Immanuel ya yi kira ga mazauna Kudancin Kaduna da su ƙara rungumar zaman lafiya da fahimtar juna.
Ya kuma taya Musulmi murna, tare da yin addu’ar Allah ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar sassan Arewacin Najeriya.
A wani ɓangare kuma, wasu malaman Musulunci, Mallam Idris Musa da Liman Ilyasu Husaine, sun nuna godiya ga shugabannin Kiristoci bisa saƙonnin goyon baya da fatan alheri da suka aiko.
Sun ce bikin Sabuwar Shekarar Musulunci ba na Musulmi kaɗai ba ne, illa na dukkan bil’adama, domin yana ɗauke da saƙon zaman lafiya da juna.
A ranar Talata 16 ga Yuni, 2026, daidai 1 ga Muharram 1447, ne ake fara sabuwar shekarar Musulunci, bisa ganin jinjirin wata.
Sabuwar Shekarar Musulunci na tunawa da Hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina, wadda ke da matuƙar muhimmanci a tarihin Musulunci.


