Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

‘Yan Sandan Gombe Sun Yi Taron Gaggawa Da Jam’iyyun Siyasa Da INEC Kan Tsaro
Published: July 18, 2026 at 2:54 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe ta gudanar da wani taron gaggawa kan harkokin tsaro tare da shugabannin jam’iyyun siyasa da wakilan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), domin tattauna yadda za a tabbatar da zaman lafiya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

An gudanar da taron ne a babban ɗakin taro na Rundunar, sakamakon ƙarin damuwa kan yawaitar laifukan da ke da alaƙa da siyasa, musamman amfani da ‘yan daba wajen tayar da tarzoma, yayin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi kafin lokacin yaƙin neman zaɓe.

Da yake maraba da mahalarta taron, Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya ce an kira taron ne bayan bayanan sirri sun nuna alamun ƙaruwa a ayyukan tashin hankali masu nasaba da siyasa tun kafin fara yaƙin neman zaɓe a hukumance.

Ya bayyana cewa matsalar Kalare da ake fuskanta a jihar, tare da nauyin da ya rataya a wuyan Rundunar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sun sa ya zama dole a haɗa masu ruwa da tsaki domin nemo mafita.

Kwamishinan ya buƙaci mahalarta taron su bayar da shawarwari masu amfani domin tabbatar da zaman lafiya, yana mai jaddada cewa lokaci mafi dacewa na dakile rashin tsaro shi ne kafin ya rikide ya gagari shawo kansa.

Shi ma da yake jawabi, Daraktan Hukumar Tsaro ta DSS a jihar Gombe, Haruna Nuhu, tare da Kwamandan Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula (NSCDC), sun bayyana taron a matsayin abin a yaba da shi kuma mai matuƙar muhimmanci.

Sun ce irin wannan zama zai ƙara bai wa hukumomin tsaro damar sa ido kan harkokin siyasa tare da tabbatar da bin dokokin zaɓe, suna mai cewa, “Idan za a yi wasan siyasa, dole ne a yi shi bisa ƙa’idoji da dokokin da aka tanada.”

A nata jawabin, Shugabar Sashen Wayar da Kan Masu Zaɓe ta INEC a Jihar Gombe, Misis Rifqatu Maxwell, ta bayyana cewa har yanzu Hukumar ba ta amince da fara yaƙin neman zaɓe ba.

Ta sanar da cewa yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa zai fara ne a ranar 19 ga Agustan 2026, yayin da na Gwamna zai fara a ranar 9 ga Satumban 2026.

Ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu da su bi ƙa’idojin INEC ba tare da karya doka ba, tana mai gargaɗin cewa duk wanda ya saɓa zai fuskanci hukuncin doka.

Shugabannin jam’iyyun siyasa da suka halarci taron sun yi alƙawarin aiwatar da matsayar da aka cimma domin tabbatar da gudanar da siyasa cikin lumana.

Daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabai akwai Manjo Janar A. K. Kwaskebe, Adamu H. Garba, Benjamin Sati, mai ba jam’iyyar PDP shawara kan harkokin shari’a, Lawan Maigoro na Jam’iyyar Labour Party da Bobo Benson Abubakar na Jam’iyyar Action Alliance.

Masu jawabin sun kuma buƙaci a magance tushen rikice-rikicen zaɓe, ciki har da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, zargin nuna son kai wajen aiwatar da dokokin zaɓe da kuma tabbatar da hukunta masu aikata laifukan zaɓe.

A nasa gudunmawar, wani Wakilin kafar yada labarai ya nuna damuwa kan ƙaruwar cin zarafi ta kafafen sada zumunta da yaɗa bayanan ƙarya a lokutan siyasa.

Ya buƙaci a ɗauki matakan kariya, ciki har da yin rajistar masu kula da kafafen yaɗa labarai na jam’iyyun siyasa da ‘yan takara a INEC, tare da tsaurara aiwatar da Dokar Laifukan Yanar Gizo (Cybercrimes Act).

A ƙarshen taron, Kwamishinan ‘Yan Sandan ya gode wa mahalarta bisa gudunmawar da suka bayar, ya kuma yi bayani kan wasu daga cikin batutuwan da aka taso da su kafin a rufe taron da ɗaukar hoton haɗin gwiwa.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Arsenal Tana Ci Gaba Da Kokarin Dauko Morgan Rogers
Next Post: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Ma’aikatan Jiha da Kwamishinoni 23

Karin Labarai Masu Alaka

SCSN Ta Yi Kira Ga Hukumomi Su Tabbatar Da Bin Doka A shari’ar El-Rufa’i Afrika
Shugaba Trump Yace Amurka Takai Hari Kharg Tsibiri a Kasar Iran Afrika
Jihar Borno Ce Tayi Nasara A Gasan Karatun Al Qur’ani Na Kasa Najeriya
Tattalin Arzikin Kasar Botswana Zai Farfado Afrika
Jirgin Sojojin Ruwa Yayi Gobara A Cross River Najeriya
APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Ummulkhairi Afrika
  • An Bukaci Mabiya Addinin Kirista Da Suyi Koyi Da Rayuwar Yesu Najeriya
  • Jami’an Tsaro Sun Dakile Safarar Makamai Daga Jos Zuwa Jihar Neja Afrika
  • Al’ummomin da Ambaliyar Ruwan Mokwa a Jihar Nejan Najeriya ta sharewa gidaje sun Koka. Najeriya
  • Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika
  • Motar Kungiyar Kwallon Kafar Bayelsa United Ta Yi Hatsari Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.