Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

SCSN Ta Yi Kira Ga Hukumomi Su Tabbatar Da Bin Doka A shari’ar El-Rufa’i
Published: September 1, 2026 at 3:46 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Majalisar Ƙoli ta Shari’a a Najeriya (SCSN) ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cikakken bin doka da oda a kan ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i.

Majalisar ta bayyana damuwa kan halin da ake ciki game da ci gaba da tsare El-Rufa’i, musamman abin da ta bayyana a matsayin wahalar cika sharuɗɗan beli da aka gindaya masa.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Majalisar, Nafiu Baba Ahmad, mni, ya fitar a ranar Litinin, Majalisar ta ce kamar kowane ɗan Najeriya, El-Rufa’i yana da haƙƙin da Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ya ba shi, kuma ana ɗaukar mutum ba shi da laifi har sai kotun da ke da hurumin shari’a ta tabbatar da hakan.

Majalisar ta jaddada cewa Najeriya ƙasa ce da ke tafiyar da tsarin dimokuraɗiyya bisa kundin tsarin mulki, inda dole ne a mutunta ka’idojin bin doka, sauraron shari’a cikin adalci da kuma tsare mutum bisa ƙa’ida, ba tare da la’akari da matsayinsa, jam’iyyarsa ko ra’ayinsa na siyasa ba.

Ta ce ba ta goyon bayan aikata laifi ko nuna ƙiyayya ga doka ta kowace hanya, amma ta ƙara da cewa neman tabbatar da adalci shi ma ya kamata ya kasance cikin adalci da bin doka.

Majalisar ta yi gargaɗin cewa duk wani mataki da ake ganin an ɗauka ba bisa ƙa’ida ba ko kuma saboda dalilan siyasa, na iya rage amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati tare da raunana tsarin dimokuraɗiyya.

Saboda haka, SCSN ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da al’amuransu cikin tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da sauran dokokin ƙasar, tare da tabbatar da cewa an bi matakan doka a kowane mataki.

Haka kuma, Majalisar ta yi kira ga hukumomi da su guji duk wani mataki da ka iya sa a zarge su da tsangwamar El-Rufa’i saboda dalilan siyasa, tana mai buƙatar a tabbatar da adalci, gaskiya da kuma bin doka.

Majalisar ta ce haɗin kan Najeriya da zaman lafiyar ƙasar na dogaro matuka da sahihancin hukumominta da kuma irin amincewar da jama’a suke da ita a kansu.

Ta jaddada cewa ba wai kawai ya kamata a yi adalci ba, har ma ya zama a bayyane ga jama’a cewa an yi adalcin, tana mai cewa yin amfani da doka cikin adalci, ba tare da nuna bambanci ba, shi ne ginshiƙin haɗin kan ƙasa da ci gaba mai ɗorewa.

Majalisar ta sake jaddada aniyarta ta kare adalci da haƙƙin ’yan ƙasa, tare da inganta zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummar Najeriya.

Ta kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kasance masu natsuwa da ɗaukar alhaki, tare da tabbatar da cewa dukkan matakai da za su ɗauka sun dace da tanadin doka.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: ’Yan Sanda, Sojoji Da DSS Sun Ceto ‘Yan NYSC Da Aka Sace A Kogi
Next Post: Lawanti Ya Ƙara Wa Gombe Daraja A Fannin Aikin Jarida – NUJ

Karin Labarai Masu Alaka

Yaki Ta Sararin Samaniya Ya Cigaba Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran Afrika
Kasar Ghana Zata Sauya Inda Take Kai Sarrafa Gwal Afrika
Mayakan M23 Sun Tsagaita Wuta A Gabashin Kwango Labarai
Kauran Gwandu Zai Inganta Wutan Lantarki A Kebbi Siyasa
Jirgin Sama Ya Fadi A Kano Labarai
‘Yan Jarida Sunyi Mummunan Hatsari A Bauchi Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Morocco Ta Kwashe ‘Yan Kasar Daga Sassan Ambaliyar Ruwa Afrika
  • Ana Zargin Tsohon Shugaban Kasar Philippines Da Ta’addaci A Lokacin Mulkinsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Trump Yace Akwai Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Iran Afrika
  • CNG Ta Farfado Da Jarin Masu Adaidaita Sahu A Kaduna Afrika
  • Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai
  • Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
  • Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Afrika
  • NAHCON Ta Fara Shirye-shiryen Dawowar Alhazai Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.