Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Ma’aikatan Jiha da Kwamishinoni 23
Published: July 18, 2026 at 5:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: July 19, 2026

Gwamnan jihar Gombe dake arewa maso Gabashin Najeriya, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rantsar da sabon Shugaban Ma’aikatan jihar, Babban Sakatare, Kwamishinoni 23 da kuma Mashawarta na Musamman, a wani mataki na ƙarfafa ayyukan gwamnati da inganta shugabanci nagari a jihar.

An gudanar da bikin rantsarwar ne a Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa ta Gombe, inda manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.

Sabon Shugaban Ma’aikatan jihar, wanda aka naɗa a watan Fabrairun wannan shekara, ya karɓi rantsuwar kama aiki a hukumance, yayin da sabbin kwamishinonin suka shiga Majalisar Zartarwar jihar bayan rusa tsohuwar majalisar a watan Afrilu sakamakon bayyana aniyar wasu daga cikin tsoffin kwamishinoni ta tsayawa takarar muƙaman siyasa.

Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce sake fasalin wasu ma’aikatu da ƙirƙirar sababbi an yi ne domin ƙarfafa hukumomin gwamnati da kuma daidaita ayyukansu da manufofin ci gaban gwamnatinsa. Ya bayyana cewa jihar yanzu tana da ma’aikatu 23 bayan kammala wannan sauyi.

Gwamnan ya bayyana sunayen kwamishinoni da ma’aikatun da aka ba su kamar haka:

Abdulkadir Mohammed Waziri – Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci.

Micah Sunday Hamman – Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki.

Farfesa Aishatu Umaru Maigari – Ma’aikatar Ilimi.

Sanusi Ahmad Pindiga – Ma’aikatar Makamashi da Albarkatun Ma’adanai.

Yusuf K. Jalingo – Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Gandun Daji.

Muhammad Gambo Magaji – Ma’aikatar Kuɗi da Bunƙasa Tattalin Arziki.

Farfesa Danladi Adamu Bojude – Ma’aikatar Lafiya.

Mohammed Saidu Mohammed – Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane.

Aishatu Mohammed Bose Ahmed – Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci.

Moses Kyari Bolda – Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Dabaru da Al’adu.

Adamu Dishi Kupto – Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida.

Zubairu Muhammad Umar – Ma’aikatar Shari’a.

Ibrahim Shehu Turaki – Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane.

Salihu Baba Alkali – Sabuwar Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo.

Sani Ahmad Haruna – Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Raya Al’umma.

Lewini Dauda Faruk – Ma’aikatar Raya Karkara da Ƙungiyoyin Haɗin Kai.

Dr Habu Dahiru – Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire.

Shehu Yerima Abdullahi – Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Haɗin Kan Yankuna.

Nasir Mohammed Aliyu – Ma’aikatar Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido.

Injiniya Bala Adams – Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.

Dakta Bertha Danja – Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a.

Dr. Usman Maijama’a Kallamu – Ma’aikatar Ayyuka da Gine-ginen More Rayuwa.

Yusuf Abdu Kwadon – Ma’aikatar Matasa da Wasanni.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa cika dukkan muhimman muƙaman gwamnati zai ƙara inganta gudanar da ayyuka da aiwatar da manufofin gwamnati cikin inganci.

Ya buƙaci sabbin jami’an da aka rantsar su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana, ƙwazo, kishin ƙasa da ɗaukar alhakin ayyukansu. Haka kuma ya ƙarfafa musu gwiwa da su yi aiki tare, su kawo sabbin dabaru wajen magance ƙalubale, tare da amfani da gogewarsu wajen ciyar da jihar gaba.

Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’ummar jihar Gombe, yana mai cewa babu wata suka marar tushe da za ta hana gwamnatin ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba.

Ya kuma gargaɗi sabbin jami’an da aka rantsar da su guji duk wani abu da zai iya tauye amincewar jama’a, tare da tabbatar da gaskiya, riƙon amana, ladabi, aiki tukuru da sadaukarwa wajen yi wa al’ummar jihar Gombe hidima.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Sandan Gombe Sun Yi Taron Gaggawa Da Jam’iyyun Siyasa Da INEC Kan Tsaro
Next Post: Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi ga Shugabannin Duniya A Taron UNGA

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Dawo Da Kudaden Ma’aikata Afrika
Sabon Babin Tsaro A Najeriya: Gombe Ta Fito Da Tsarin Smart Security Na Farko Afrika
Hukumar Zabe A Kasar Honduras Ta Sanar Da Nasry Asfura A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Ƙasa Afrika
Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo Labarai
Shugaba Bola Tinubu Ya Saka Hannu A Dokar Zabe Najeriya
Shugaban Amurka Yace Zayyi Wahala A Cimma Yarjejeniya Tsakanin Isra’ila, Amurka Da Iran Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ana Cigaba Da Jimamin Rasuwar Mataimakin Gwamnan Bayelsa Najeriya
  • CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika
  • Gombe Ta Yi Fice A Duniya: Maryam Dan’azumi Ta Lashe Gasar Alƙur’ani Na Ƙasa Da Ƙasa Afrika
  • Harin Makami Mai Linzami Da Rasha Ta Kai Yayi Barna Sosai A Ukraine Afrika
  • Hatsarin Mota Yayi Ajalin Mutum 7 A Gombe Najeriya
  • ‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.