Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Shugaba Trump Ya Jinjinawa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya
Published: July 22, 2026 at 5:05 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa abin da ya bayyana a matsayin jajircewarsa wajen jagorantar Najeriya da kuma ƙoƙarin magance matsalolin tsaro, musamman hare-haren da ke shafar wasu al’ummomin Kiristoci.

A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Yulin 2026 da ya aike wa Shugaba Tinubu, Trump ya yaba da ƙudurin shugaban na yaƙi da ta’addanci tare da tabbatar da cewa Amurka za ta ci gaba da mara wa Najeriya baya wajen inganta tsaro da tabbatar da zaman lafiya.

Trump ya ce abin alfahari ne gare shi ya tsaya tare da Shugaba Tinubu wajen yaƙi da ‘yan ta’adda, yana mai bayyana cewa haɗin gwiwar ƙasashen biyu zai taimaka wajen ƙarfafa Najeriya da bunƙasa tattalin arzikinta.

Shugaban na Amurka ya ce Najeriya da Amurka suna da manufar bai ɗaya ta yaƙi da ta’addanci a yankin Yammacin Afirka, yana mai nuni da cewa Tsarin Haɗin Gwiwar Tsaro na Amurka da Najeriya na shekarar 2026 ya samar da ingantaccen tubali na zurfafa haɗin gwiwar soji tsakanin ƙasashen biyu.

Ya kuma bayyana cewa Amurka ta tura jami’an rundunar musamman domin horas da sojojin Najeriya tare da ba su ƙwarewa, bayanan sirri da sauran tallafin da za su taimaka wajen yaƙi da ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Trump ya kuma bayyana fatan ci gaba da tattaunawa da Shugaba Tinubu domin ƙara bunƙasa alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Amurka.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: An Gabatar Da Sabbin Kudurorin Kare Muhalli Da Gandun Daji A Gombe
Next Post: Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwar da Mutane a Jihar Gombe Tsaro
‘Yan Ta’adda Sun Hallaka Malaman Makaranta A Tilabery Afrika
Mali Da Burkina Faso Za Su Haramta Wa Amurkawa Izinin Shiga Ƙasashen Su Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sojojin Isra’ila Sun Kashe Babban Kwamandan Kungiyar Hezbollah Afrika
Mutane 27 Sun Rasa Rayukan Su A Najeriya Afrika
Thailand Da Cambodia Sun Fara Tattauunawa Kan Batun Tsagaita Wuta Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Nuhu Ribadu Ya Mika Yara 130 Da Aka Kubutar Ga Gwamna Bago Tsaro
  • Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
  • Kauran Bauchi: Muna Nan A PDP Daram! Siyasa
  • Chadi Ta Sauyawa ‘Yan Gudun Hijira Matsuguni Afrika
  • Tinubu Ya Kawo Ƙarshen Aikin Kwamitin Sayar Da Kaddarorin Gwamnati Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane Takwas Da Ake Zargi Da Siyar Da Tikitin AFCON Ba Bisa Ka’ida Ba Wasanni
  • Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
  • Tattalin Arzikin Najeriya Ya Karu A Karshen 2024 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.