Gwamnatin jihar Gombe tare da haɗin gwiwar Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), sun ƙaddamar da shirin Kwanaki 1,000 na Farko, da nufin kare yara daga tamowa ta hanyar ƙarfafa kula da lafiyar uwa da jariri tun daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa lokacin da yaro ya cika shekara biyu.
Shirin, wanda zai gudana na tsawon shekara guda tare da tallafin ƙungiyar Latter-day Saints Charities, na da manufar inganta abinci mai gina jiki ga mata masu juna biyu da yara, ta hanyar ƙarfafa tsare-tsare, samar da isassun kuɗaɗe, inganta haɗin gwiwa, tabbatar da bin diddigi da kuma wayar da kan al’umma.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin a Gombe, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Gombe, Dr. Abdulrahman Shuaibu, ya bayyana shirin a matsayin wata muhimmiyar zuba jari ga lafiyar yara da makomar ci gaban jihar.
Ya ce tamowa na ci gaba da yin illa ga girman yara, bunƙasar ƙwaƙwalwarsu, ƙwarewar koyo da kuma irin gudummawar da za su bayar wajen ci gaban al’umma a nan gaba.
A cewarsa, rigakafin tamowa ya kamata ya fara tun kafin haihuwa, ta hanyar tabbatar da ingantacciyar kulawa ga mata masu juna biyu, haihuwa cikin aminci, shayar da jarirai nonon uwa kaɗai na tsawon watanni shida na farko, da kuma ba su ƙarin abinci mai gina jiki da ya dace bayan wannan lokaci.
Dr. Abdulrahman ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin jihar Gombe na ci gaba da aiki tare da abokan hulɗa na ci gaba domin ƙarfafa ayyukan inganta abinci mai gina jiki da kuma rage mace-macen yara a faɗin jihar.
A nata jawabin, Shugabar Ofishin UNICEF na Bauchi, Dr. Nuzhat Rafique, ta ce shirin ya nuna ƙudurin bai ɗaya na tabbatar da cewa kowace uwa da kowane yaro a Gombe ba wai kawai suna rayuwa ba, har ma suna samun damar bunƙasa cikin ƙoshin lafiya.
Ta bayyana cewa kwanaki 1,000 na farko na rayuwar ɗa su ne mafi muhimmancin lokaci wajen bunƙasar ƙwaƙwalwa, girman jiki, ƙarfin garkuwar jiki da kuma lafiyar mutum na tsawon rayuwarsa. Ta ce duk wata zuba jari da aka yi a wannan lokaci na samar da gagarumar riba wajen bunƙasa jarin ɗan Adam.
Dr. Rafique ta ce shirin ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da Nutrition 774 Initiative, tsarin Health Sector-Wide Approach, da kuma National Food and Nutrition Policy.
Ta ce shirin zai mayar da hankali kan inganta tsare-tsaren da suka dogara da hujjoji, ƙarfafa haɗin gwiwa da samar da kuɗaɗe don shirye-shiryen inganta abinci mai gina jiki, bunƙasa tsarin kiwon lafiya da samar da abinci, da kuma wayar da kan iyalai kan hanyoyin ciyar da mata masu juna biyu, jarirai da ƙananan yara yadda ya kamata.
Ta jaddada cewa bai kamata a bari yaro ya kamu da tamowa ba, domin idan hakan ta faru, wasu daga cikin illolin da ke shafar bunƙasar ƙwaƙwalwa da makomarsa ba sa iya komawa yadda suke.

Haka kuma, ta ce shirin zai taimaka wajen inganta lafiyar mata masu juna biyu, ƙara yawan shayar da jarirai nonon uwa kaɗai, inganta ciyar da yara ƙarin abinci mai gina jiki, hana ƙarancin sinadaran gina jiki a jiki, da kuma ƙarfafa ayyukan kula da abinci mai gina jiki a matakin al’umma.
Ta yi kira ga gwamnati, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ƙungiyoyin farar hula, abokan hulɗa na ci gaba da kuma al’umma su ci gaba da saka hannun jari wajen yaƙi da tamowa, ƙara kasafin kuɗi, tabbatar da bin diddigi da kuma ƙarfafa iyalai su rungumi ingantattun hanyoyin ciyar da mata masu juna biyu da yara.
Har ila yau, ta buƙaci kafafen yaɗa labarai su mayar da hankali kan yaɗa rahotannin da ke ƙarfafa rigakafin tamowa da kuma sauya ɗabi’un al’umma ta fuskar ingantaccen abinci.
Ita ma Kwararriyar UNICEF kan harkokin abinci mai gina jiki, Philomena Irene, ta bayyana cewa kwanaki 1,000 na farko wata dama ce ta musamman da ba ta maimaituwa wajen tabbatar da lafiyar yaro har tsawon rayuwarsa.
Ta ce wannan lokaci, wanda ya fara daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa lokacin da yaro ya cika shekara biyu, shi ne mafi dacewa wajen hana tamowa da kuma karya da’irar talauci da rashin daidaito.

A cewarta, kashe kusan Naira dubu 21 wajen rigakafin tamowa ga kowane yaro ya fi araha idan aka kwatanta da kusan Naira dubu 190 da ake kashewa wajen kula da yaron da ya kamu da matsananciyar tamowa.
Masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun bayyana fatan cewa wannan shiri zai ƙarfafa ayyukan inganta abinci mai gina jiki, bunƙasa yadda ake kula da lafiyar uwa da yaro, ƙara sa hannun al’umma, tare da rage yawan tamowa da mace-macen yara a Jihar Gombe.


