Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Maulidi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu
Published: August 21, 2026 at 1:34 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 25 ga Agustan 2026, a matsayin ranar hutu a Kasar domin bikin Maulidi wato zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW)

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin kasar inda ya taya Musulmi a Najeriya da sauran ƙasashen duniya murnar zagayowar ranar.

Ministan ya ce Maulidi na ba da damar yin tunani kan darussan da ake samu daga rayuwar Annabi, musamman tausayi da hidima ga sauran mutane, yana mai cewa waɗannan halaye na daga cikin abubuwan da Najeriya ke matuƙar buƙata a yanzu.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, tare da gudanar da bikin cikin natsuwa da mutunta juna.

Tunji-Ojo ya tabbatar da aniyar Gwamnatin Tarayya na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa da tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Dan Wasan Gaba Na Manchester United, Zirkzee Ya Amince Da Komawa Juventus Ko Napoli
Next Post: FIFA Ta Buɗe Bincike Kan Koci Hossam Hassan Na Masar

Karin Labarai Masu Alaka

Meyasa Israela Take Hana Kaiwa Gaza Kayan Tallafi Afrika
Yau Litinin Ake Cigaba Da Shari’ar Najib Zarak Labarai
Anyi Bikin Cikar Tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami Shekaru 84 Afrika
Ingila, Hauhawar Farashi Yayi ƙasa Sosai Labarai
Zamfara: Sai Mun Hada Kai Don Kawo Karshen Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Umarci Janye ‘Yan Sanda Masu Gadin Ministoci Tsaro
  • Amurka Ta Cire Takunkumin Da Ta Kakabawa Shugaban Venezuela Amurka
  • Gwamnatin Kasar Benin Ta Nemi ‘Yan Kasa Su Kwantar Da Hankali Afrika
  • Shugaban Najeriya Tinubu Ya Amince Na Tura Jakadu Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Jinjinawa Saudiya Afrika
  • Amurka Ta Gabatarwa Sassan Dake Yakar Juna A Sudan da Shirin Tsagaita Wuta Afrika
  • Guinea An Zabi Madugun Sojojin Da Suka yi Juyin Mulki Mamady A Shugaban Ƙasar, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Roger Lumbala Shekaru 30 Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.