Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika
  • Yara Miliyan 16 Sun Amfana Da Azithromycin A Karkashin Shirin SARMAAN Afrika

Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
Published: September 10, 2026 at 3:29 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya rantsar da sabbin manyan  Sakatarorin guda 19, matakin da ya zama naɗe-naɗen Sakatarorin Dindindin mafi yawa da aka taɓa yi a lokaci guda a tarihin jihar.

Yayin gudanar da bikin rantsarwar a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa da ke Gombe, gwamnan ya ce sabon naɗe-naɗen ya kawo adadin Sakatarorin Dindindin da gwamnatinsa ta nada zuwa 55 cikin shekaru bakwai da rabi da ta yi tana mulki, baya ga daraktoci sama da 100 da aka ɗaga zuwa manyan matakan gudanarwa na ma’aikatan gwamnati.

Ya ce naɗe-naɗen wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa hukumomin gwamnati, cike gibin ƙarancin ma’aikata da kuma gina ƙwararrun ma’aikatan gwamnati da za su iya ci gaba da tafiyar da ayyukan ci gaba ko bayan wa’adin mulkinsa.

Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da gwamnan ya bayyana shi ne cewa gwamnatinsa na shirin gudanar da gagarumin aikin ɗaukar sabbin ma’aikata a ma’aikatan gwamnati na jihar, bayan kafa sahihin kundin bayanan ma’aikata ta hanyar tsarin tantance ma’aikata da na’urar zamani ta biometric.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce ya riga ya umarci Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na jihar da ya haɗa kai da Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar wajen gudanar da cikakken bincike kan buƙatun ma’aikata a ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati, domin gano gibin da ake da shi da kuma adadin ma’aikatan da ake buƙata.

Ya ce wannan aiki zai share fagen ɗaukar sabbin ma’aikata kafin wa’adin mulkinsa ya ƙare a ranar 29 ga Mayun 2027.

A cewarsa, tsarin tantance halartar aiki da tabbatar da bayanan ma’aikata ta hanyar biometric, wanda ya fuskanci suka lokacin da aka ƙaddamar da shi, ya nuna muhimmancinsa, domin ya bai wa gwamnati sahihan bayanai kan ainihin yawan ma’aikatan da ke aiki.

Ya ce tsarin ya kuma taimaka wajen yaƙi da ma’aikatan bogi da kuma rashin halartar aiki, tare da ceton jihar biliyoyin nairori.

Gwamnan ya bayyana cewa gyare-gyaren sun kuma samar da ginshiƙin da ake buƙata domin gudanar da ɗaukar ma’aikata bisa haƙiƙanin buƙata da kuma adalci.

Ya ce tun bayan da ya hau mulki, gwamnatinsa ta sanya gyaran ma’aikatan gwamnati da ƙarfafa hukumomi cikin abubuwan da ta fi ba muhimmanci, yana mai nuni da kafa Hukumar Gyaran Ayyukan Ma’aikatan Gwamnati (Bureau for Public Service Reforms) a matsayin wani muhimmin mataki na inganta aiki, riƙon amana da samar da ingantaccen aiki ga jama’a.

Baya ga batun ma’aikata da gyaran hukumomi, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce walwalar ma’aikata na daga cikin muhimman manufofin gwamnatinsa.

Ya kawo biyan albashi a kan lokaci, aiwatar da mafi ƙarancin albashi a matakin jiha da ƙananan hukumomi, ƙarin girma na ma’aikata akai-akai, da kuma biyan bashin fansho da garatuti, a matsayin hujjojin da ke nuna ƙudirin gwamnati na kula da jin daɗin ma’aikata da waɗanda suka yi ritaya.

Dangane da bashin garatuti, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta biya sama da naira biliyan 33 a cikin shekaru bakwai da rabi da ta yi tana mulki, inda ya ce kusan kashi 70 cikin 100 na bashin da aka biya ya fito ne daga bashin da gwamnatin da ta gabata ta gada.

Ya sanar da cewa za a sake biyan wani kaso na kuɗaɗen garatuti kafin ƙarshen watan Satumban 2026, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnati za ta kammala biyan duk sauran bashin garatuti kafin ƙarshen zangon farko na shekarar 2027.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnati ta kuduri aniyar barin ma’aikatan gwamnati da suka fi ƙwarewa, masu bin diddigin ayyukansu ta hanyar tsarin zamani, isassun ma’aikata, kuma masu iya amsa buƙatun al’umma yadda ya kamata.

Dangane da yadda aka zaɓi sabbin Sakatarorin Dindindin, gwamnan ya ce an tsara tsarin ne domin tabbatar da cancanta, ƙwarewa da kuma adalci wajen wakilcin al’ummomi daban-daban.

Ya bayyana cewa an yi la’akari da manyan daraktoci daga ƙananan hukumomin jihar, inda aka binciki cancantarsu, ƙwarewarsu da tarihin aikinsu.

An kuma gudanar da rubutaccen jarabawa domin tantance iliminsu na gaba ɗaya da kuma ƙwarewarsu a fannin fasahar sadarwa da bayanai, wato ICT.

Ya ƙara da cewa biyu daga cikin sabbin Sakatarorin Dindindin an ɗauke su ne daga wajen tsarin ma’aikatan gwamnati na jihar, inda ɗaya ya fito daga Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, ɗayan kuma daga jami’o’i, domin kawo ƙarin ƙwarewar gudanarwa, haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma sabbin dabarun bincike cikin ma’aikatan gwamnatin jihar.

Gwamnan ya buƙaci sabbin Sakatarorin Dindindin da su ɗauki naɗe-naden nasu a matsayin babban nauyi da aka ɗora musu, ba wai wata nasara ta kansu kawai ba.

Ya ce: “Ku ne jakadun ma’aikatan gwamnati da kuma al’ummominku. Naɗin da aka yi muku ba nasara ce ta kanku kaɗai ba; amana ce da al’ummar Jihar Gombe suka ɗora muku.”

Ya buƙace su da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana, ladabi da himma, yana mai gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da cin hanci da rashawa, rashin da’a, rashin gaskiya ko amfani da ofis wajen cin zarafi ba.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce yayin da gwamnatinsa ke shiga zangon ƙarshe na wa’adinta, za a mayar da hankali ne kan ƙarfafa gyare-gyaren da aka fara, ƙarfafa hukumomi da kuma tabbatar da cewa nasarorin da aka samu a tsawon shekaru sun dore bayan ƙarshen wannan gwamnati.

Tun da farko, Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya bisa jagorancinsa mai ma’ana, wanda ya kasance yana ba ƙwarewa, cancanta, riƙon amana da bunƙasa hukumomi muhimmanci.

Farfesa Njodi ya tabbatar wa gwamnan cewa ma’aikatan gwamnati za su ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa manufofin gyaran gwamnati da shirye-shiryen ci gaban jihar.

Ya taya sabbin Sakatarorin Dindindin murna, tare da buƙatar su kasance masu kusanci da jama’a, sauraron buƙatunsu da kuma ƙirƙirar sabbin hanyoyin inganta ayyukansu.

Da yake jawabi a madadin sabbin Sakatarorin Dindindin, Musa Mohammed Babaji ya gode wa Gwamna Inuwa Yahaya bisa amincewar da ya nuna musu, yana mai alƙawarin cewa waɗanda aka naɗa za su tabbatar da sun cancanci wannan amana ta hanyar ƙwazo, biyayya, ƙwarewa da jajircewa wajen samar da ingantaccen aikin gwamnati.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
Next Post: ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi

Karin Labarai Masu Alaka

Wani Bincike Ya Nuna Cewar Da Wuya Iran Ta Bude Mashigin Hormuz Afrika
Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika
NANPAN Ta Wayar Da Al’umma Kan Amfanin Shayar Da Jarirai Nono Kaɗai Afrika
An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau Afrika
Shugabannin Kiristoci Sun Halarci Filin Idi A Kaduna Domin Nuna Haɗin Kai Afrika
Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sakataren Kungiyar NATO Yayi Magana Da Hukumomin Kasashe Afrika
  • Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gidauniya: An Fara Tiyatar ‘Hernia’ Da ‘Hydrocele’ Kyauta A Jihar Katsina Labarai
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000 Najeriya
  • An Maka Wasu Jami’an Immigration A Kotu Bisa Zargin Rashin Da’a A Birtaniya Labarai
  • Farashin Dalar Amurka Ya Tashi Ranan Juma’a Amurka
  • Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.