Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Kebbi Ta Ce Sama Sa Maniyyata 3,000 Ne Suka Biya Naira Biliyan 21.5 Na Kujerun Hajji Afrika
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya Afrika
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91 Afrika
  • Filato: Gwamnati Ta Ƙarfafa Matakan Kariya Yayin Sake Buɗe Makarantu Afrika

Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini
Published: September 15, 2026 at 9:48 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Sokoto ta nesanta kanta daga duk wani mutum ko ƙungiya da ke fakewa da addini wajen batanci ko cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW), iyayensa, iyalansa da sahabbansa.

Gwamnatin ta bayyana cewa tana ci gaba da jaddada cikakken biyayyarta, girmamawarta da mutuntawa ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), da kuma iyalansa da sahabbansa.

A cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnatin jihar Sokoto, Abubakar Bawa, ya sanya wa hannu a fadar gwamnatin jihar a ranar 15 ga Satumba, 2026, gwamnatin ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da nuna ƙauna, girmamawa da mutuntawa ga Annabi Muhammad (SAW).

Sanarwar ta zo ne bayan tashin-tashinar da ta faru a wasu sassan babban birnin Jihar Sokoto, wadda ake alakanta ta da batun addini.

Dangane da lamarin, gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti na malamai domin gudanar da bincike kan musabbabin rikicin, tare da bai wa gwamnatin shawarwari kan matakan da suka dace a ɗauka domin kare martaba da maslahar jihar.

Haka kuma, gwamnatin ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kai da kuma kisan da ya faru a Masallacin Juma’a na Musa Lukuwa da ke Mabera.

Gwamnatin ta kuma bayar da umarnin rufe masallacin har zuwa wani lokaci, kasancewarsa wurin da aka aikata laifin, domin ba da damar gudanar da bincike kan lamarin.

A wani ɓangare na sanarwar, gwamnatin ta yi kira ga al’ummar jihar da su guji furta kalamai masu tayar da hankali ko waɗanda za su iya rura wutar rikici da tunzura jama’a.

Ta ce irin waɗannan kalamai na iya kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma, waɗanda ta ce jihar Sokoto ta shahara da su.

Gwamnatin ta kuma tabbatar wa al’ummar jihar da cikakken kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

Ta buƙaci jama’a da su ba jami’an tsaro da hukumomin da ke gudanar da bincike cikakken haɗin kai, tare da kauce wa duk wani mataki da zai iya ƙara dagula al’amura.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kebbi Ta Ce Sama Sa Maniyyata 3,000 Ne Suka Biya Naira Biliyan 21.5 Na Kujerun Hajji

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Najeriya Zata Rabawa Al’umma Tallafin Noma Afrika
Najeriya Tayi Asarar Kusan Naira Triliyan 1 Sakamakon Harajin Trump Amurka
Ghana Ta Haramta Hakar Ma’adinai A Gandunan Dajin Data Kebe, Labarai
Kanal Sani: Idan ‘Yan-Ta’adda Zasu Mutunta Sulhu To Gwamnati Ta Duba Hakan Labarai
Amurka Da Isra’ila Sunkai Hari Kan Iran Amurka
Sarkin Gombe Ya Ziyarci Gwamna Inuwa Yahaya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Malamai Don Binciken Rikicin Addini
  • Kebbi Ta Ce Sama Sa Maniyyata 3,000 Ne Suka Biya Naira Biliyan 21.5 Na Kujerun Hajji
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Bamanga Tukur, Sun Yaba Da Gudunmawarsa Ga Najeriya
  • Tsohon Shugaban PDP, Bamanga Tukur, Ya Rasu Yana da Shekaru 91

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rundunar Operation Hadinkai Sunyi Nasara Akan ISWAP Da Boko Haram Najeriya
  • Ministan Kudin Botswana Yace Akwai Hasashen Cewa Tattalin Arzikin Kasar Zai Ragu Amurka
  • Kasar Amurka Takara Saka Takunkumi Akan Kasar Venezuela Amurka
  • Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz Amurka
  • Majalisar Wakilai Ta Rikon Kwaryar Nijar Ta Gudanar Da Zama Karo Na Biyu Afrika
  • An Tsaurara Tsaro Yayin Da Tehran Ke Shirin Karɓar Masu Jimamin Ayatollah Khamenei Afrika
  • Tattalin Arzikin Kasar Bahrain Ya Bunkasa Sakamakon Ruruwar Masu Yawon Bude Ido Labarai
  • Nuhu Ribadu Ya Mika Yara 130 Da Aka Kubutar Ga Gwamna Bago Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.